GWAMNATIN ZAMFARA NA CIGABA DA LALUBEN HANYOYIN DAKILE JEFI-JEFI NA SATAR SHANUN DA NA YI SAURA A JAHAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 17 January 2020

GWAMNATIN ZAMFARA NA CIGABA DA LALUBEN HANYOYIN DAKILE JEFI-JEFI NA SATAR SHANUN DA NA YI SAURA A JAHAR.

A Cigaba da yunkurinta na kawo karshen satar shanu a jahar Zamfara. Gwamnatin jahar na cigaba da laluben hanyoyin da za su kawo karshen dukkanin burbushin matsalar tsaro, satar shanu da kuma garkuwa da mutane, a jahar.

Hakan ya sa Kwamishinan Ma'aikatar tsaro da Lamuran cikin Gida na jahar Hon. Abubakar Muhammad Dauran Justice. Ya ke cigaba da tattaunawa da bangarorin da ke da ke da ruwa da tsaki akan wannan matsalar.

Wanda ya sa Kwamishinan ya gana sarakunan Zango na dukkanin kasuwannin jahar da masu daukar shanu Hoto, a ofishinsa.

Inda su ka tattauna akan hanyoyin da bangarorin za su taimaka domin dakile satar shanu. Musamman ganin irin muhimmanci da su ke da shi, domin Sai an sayi shanun, masu satar za su ji karfin cigaba da satar.

Wanda shuwagabannin bangarorin su ka jaddada bayar da goyon bayansu ga yunkurin gwamnatin jahar Zamfara na Samar da tsaro ta hanyar dakile duk wani yunkuri na saye da sayar da shanun sata a karorin shanu na jahar Zamfara.

Haka Zalika a wajen taron an bullo da wasu sabbin hanyoyin da za su taimaka wajen magance saye da sayar da shanun satar.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State17th January, 2020


Post Bottom Ad

Responsive Ads Here