Da farko dai shugaban ya ziyarci fadar Mai Martaba 'Yan Doton Tsafe Alhaji Muhammad Bawa, domin neman tubarraki, haka Zalika shugaban ya shiga Kwalejin, Inda ya samu kyakkyawan tarba daga malamai da ma'aikatan makarantar. Daga nan ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru domin tabbatar da cigaban makarantar tare da tabbatar da duk wasu kalubalai da makarantar ke fuskanta sun zama tarihi. Haka Zalika shugaban ya tabbatar da cewa zai yi aiki tukuru ba tare da sani ko sabo ba, don cigaban makarantar.
Haka Zalika shugaban ya zagaya a lungu da sako na Kwalejin da su ka hada da ajizuwan karatu, assibitin makarantar, sashen na'urori masu kwakwalwa tare da sashen Lura da hakori, Inda ya ga halin da su ke ciki. Tare da alkawarin zai yi iya yinsa na ganin cewa wadannan matsalolin sun zama tarihi. Ta hanyar yin wasu ayukkan da ya ke iyawa wadanda su ka SHA karfinsu zai Kai su ga mai girma Gwamna domin tabbatar da an samu cigaba Mai dorewa, a makarantar.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
8-1-2020
