KUNGIYAR BMM LEADERSHIP FORUM TA GUDANAR DA TARONTA NA FARKO MATAKIN JAHA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 11 January 2020

KUNGIYAR BMM LEADERSHIP FORUM TA GUDANAR DA TARONTA NA FARKO MATAKIN JAHA.

Wannan kungiyar da aka kirkira  da manufar yada manufofin Gwamnatin Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, a kafafen Sada zumunta.

Shugaban kungiyar na jahar Zamfara, Aminu Waksong Maradun ya bayyana cewa sun kafa wannan kungiyar ne, da manufar yada kyawawan manufofin Gwamnatin jahar Zamfara. Wanda haka ya sa ya ga ya cancanta ya gayyato matasa masu hazaka a duk fadin jahar Zamfara domin yin aiki Kasa-rika. 

Da ya ke jawabi shugaban kungiyar Zasmo na jahar Zamfara Hon. Alhaji Ibrahim Bello Gusau (IBG) ya yi wa mahalarta taron bita akan wasu Dabi'u da halaye da ya kamata su rika domin cin nasarar wannan aiki nasu, haka Zalika ya zayyano wasu daga cikin dabi'u da ya kamata su gujewa Dan gudun aikata ba daidai ba a kafafen Sada zumunta.

Da ya ke jawabi uban wannan kungiyar Alh. Abubakar Ja'afar Maradun (PPS) Wanda Alh. Ibrahim Bello (Alhajin Apc) ya wakilta, ya Karfafawa yayan kungiyar tare da shawartarsu da su zage damtse wajen yayata kyawawan manufofin wannan gwamnatin. Haka Zalika ya bayyana cewa a matsayinsa na Masoyin Gwamnantin Barden Hausa, zai zamar masu uba na gari wajen share masu dukanin kukansu daidai iya karfinsa.

Taron da ya gudana a dakin baki na Faila Restaurant da ke sabuwar Kasuwa Gusau. Ya samu halarta, dukkanin Shuwagabannin kungiyar na jahar Zamfara.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

11-1-2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here