A kokarin gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun na cike gibin da jahar ta ke da shi na karancin kwararru a bangaren kiyon lafiya da kyere-kyere. Ya sa gwamnatin ta zakulo 'ya'yan Talakawa masu hazaka har 200 Karkashin kulawar Mai bashi shawara na musamman Hon. Lukman Majidadi. Inda ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen Sudan, India Cyprus da kuma China.
Wadannan Dalibbai da su ka hada da maza da mata, za su karancin Ilimin likitanci (Medicine) jinya (Nursing) Kwamfuta da kuma injiniyanci da sauransu.
Wanda tuni Dalibbai 66 sun isa a kasar Sudan a watan da ya shude. Haka Zalika yau mutum 23 sun sauka a kasar India. Inda suka kama 89 kenan.
Sauran 111 da za su tafi kasar China da Cyprus kuma ko yaushe daga yanzu za su bar Najeriya domin cigaba da karatunsu.
Idan dai ba a manta ba, tun da wannan gwamnatin ta Barden Hausa ta hau karagar mulki, ta Fara daukar matakai na bunkasa sha'anin ilimi Wanda Hakan ya sa jahar ta yi nasarar biyan sama na kashi saba'in na basukkan da Waec da Neco ke biyar jahar Zamfara Wanda ya haifar da nasarar samun nasarar cin jarabawar waec da kashi 72 cikin Dari, Wanda shi ne Karon farko da aka samu nasarar jarabawar kamar haka tun bayan kirkirar jahar a 1996.
Abdulmalik Saidu Maibiredi Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
14th January,2020
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Tuesday, 14 January 2020
Home
Unlabelled
DALIBBAI 89 CIKIN 200 DA GWAMNATIN ZAMFARA TA DAUKI NAUYIN KARATUNSU SUN ISA KASASHEN SUDAN DA INDIYA.
DALIBBAI 89 CIKIN 200 DA GWAMNATIN ZAMFARA TA DAUKI NAUYIN KARATUNSU SUN ISA KASASHEN SUDAN DA INDIYA.
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

