GWAMNATIN ZAMFARA TA KOYAWA MATA MASU DAUKE DA CUTAR SIDA (HIV/AIDS) SANA'O'I TARE TALLAFA MASU DA KUDADE - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 20 February 2020

GWAMNATIN ZAMFARA TA KOYAWA MATA MASU DAUKE DA CUTAR SIDA (HIV/AIDS) SANA'O'I TARE TALLAFA MASU DA KUDADE












A cigaba da yunkurinta na tallafawa Al'ummar jahar, Gwamnatin Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ta shirya shirin koyawa mata masu dauke da cuta Mai karye garkuwar jiki (HIV/AIDS) sana'o'in hannu da su ka hada da: Air Freshener, Man shafawa, da man kitso. tare da baiwa dukkanin matan tallafin naira dubu goma-goma (10,000) bayan kammala karbar horon.

Wadannan matan dai dukkaninsu Suna dauke da wannan cuta, kuma an zakulo su ne, daga kananan hukumomin jahar goma sha hudu.

Da yake jawabin Project Manager na wannan ma'aikatar ZAMSACA Aminu Dan-wada tun bayan hawan wannan gwamnatin ne, mu ka koka mata halin da masu dauke da wannan cuta su ke fama da rashin ayukkan yi. Hakan ya sa Mai girma Gwamna Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya ba mu wadannan kudaden domin mu tallafawa wadannan mata. Don haka muka shirya wannan koyarwar ga wadannan bayin Allah saboda karfafa masu guiwa su rayu kamar kowa tare da tabbatar da cewa ba su zama cima kwance ba, saboda yunwa kurrum wani ciyo ne, Mai zaman kansa. Fiye da ita wannan cutar baki daya.

Haka Zalika ya Kara da cewa sun ji dadin wanann gudunmawa da su ke samu daga gwamnatin jahar Zamfara. Wanda ya bayyana sun yi shekaru ba su samu ba, musamman gwamnatin da ta gabata.

Shugaban ya yi kira ga wadanda su ka amfana da horarwa da wadannan kudade, da su yi amfani da su wajen jan jari domin samun abin da su ka ci, kasancewar Suna samun magani kyauta.

Da su ke jawabi wadanda su ka amfana sun nuna matukar jin dadinsu da wannan horo da su ka samu, tare da alkawarin cewa za su zama jakadu na gari wajen yaki da wannan cutar tare da tabbatar sun zama masu dogaro da Kai domin su rayu kamar kowa.

Haka Zalika sun yi godiya ga gwamnatin jahar Zamfara, akan wannan gudunmawa ta ba su Wanda su ka bayyana da ba su taba samun gwamnatin da ta rungume su kamar wannan ba.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
20th February 2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here