SAMA DA MUTUM DARI TAKWAS SUN AMFANA DA TALLAFI DAGA KWAMISHINAN TSARON ZAMFARA A GARIN ZURMI.* - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 29 February 2020

SAMA DA MUTUM DARI TAKWAS SUN AMFANA DA TALLAFI DAGA KWAMISHINAN TSARON ZAMFARA A GARIN ZURMI.*







A cigaba da yunkurinsa na ganin ya bi umurnin Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun na duk Mukarabansa su tashi tsaye domin tallafawa Al'umma. Don yakar talaucin da Al'ummar jahar Zamfara ke fama da shi.

Kwamishinan tsaro da ayukkan cikin gidan jahar Zamfara, Hon. Abubakar Muhammad Dauran Justice, ya kaddamar da tallafawa masu Dan karamin karfi har sama da Dari Takwas a karamar hukumar Zurmi a jahar Zamfara. Abubuwan da aka raba sun hada da suturu ga maza da mata da kuma kungiyar Fulani da shuwagabannin Jam'iyar PDP na karamar hukumar . Tare da malaman Addini da kuma limamai da su ka amfana da kuma Alkur'anai masu girma ga dukkanin makarantannin addinin da ke gundumar. Da kuma kudade. Sai kuma Dalibbai 18 da ya dauki nauyin karatunsu a Kwalejin kimiya da fasaha da ke Gusau (Zacas) domin su yi karatun diploma

Da ya ke jawabi Kwamishinan tsaron ya bayyana cewa ya yi wannan shirin ne, domin tallafawa masu Dan karamin Karfi Kamar yadda mai girma Gwamna ya umurce su da su yi.

Haka Zalika Kwamishinan ya bayyana cewa zai yi irin wannan shirin kamar yadda ya yi shi a Dauran sai yau kuma ya yi a Zurmi, zai karade dukkanin Yankuna uku na karamar hukumar Zurmi da wasu yankuna na jahar Zamfara, domin tabbatar da Al'umma sun samu saukin rayuwa. Kari akan hakan Kwamishinan ya yi amfani da wannan damar Inda ya yi kira ga 'yan uwa fulani da su cigaba da zaman lafiya tsakaninsu da Hausawa.


Da ya ke jawabi a madadin mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara, Tsohon kantoman Soji na jahar Nasarawa Kanal Bala Mande (mai Ritaya)  ya yi jinjina ga wannan Kwamishinan, tare da shawartarsa da ya rike wannan kyakkyawan aiki domin tallafawa Al'umma. Haka Zalika ya shawarci sauran 'Yan siyasa da su yi koyi da wannan dan tahaliki.


Bikin raba kayan dai ya samu halartar Kwamishinan Ma'aikatar Yada Labarai da Al'adu da yawon Buda ido Hon. Sulaiman Tunau Anka da sauran manyan Yan siyasar karamar hukumar Zurmi Malamai, uwayenmu mata da matasa da sauran Al'umma.


Abdulmalik Saidu Maibiredi

19-2-2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here