A cigaba da yunkurinta na ganin ta kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara. Karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun. Ta bullo da shirin sulhu a jahar Zamfara, Wanda shi ne silar shawo kan matsalar tsaron da ke addabar jahar.
Taron Wanda ya gudana a fadar Mai Martaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda Alh. Muhammad Ahmad Asha (MFR) karkashin jagorancin Kwamishinan tsaro da ayukkan cikin gidan jahar Zamfara Hon. Abubakar Muhammad Dauran Justice, zaman Wanda ya kunshi dukkanin uwayen kasar Kaura Namoda, sarakunan Fulani da ardo-ardo na karamar hukumar. An tattauna akan matsaloli jefi-jefi da ke fuskantar yankin da kuma yadda za a hada kai domin ganin an magance dukkan matsalolin da ke yankin. Daga karshe dukanin bangarorin sun yi jawabai masu ratsa zuciya tare da alkawarin cewa za su zama jakadun kirki wajen Samar da tsaro a jahar.
Da ya ke jawabi Kwamishinan tsaron ya yi Kira ga 'Yan uwa Fulani Hausawa da su dawo da halin kirki da mutunci da aka sansu da shi. Ta hanyar zama lafiya da junansu tare da yin godiya akan hadin kai da aka samu tsakanin Fulani da Hausawan. Daga karshe yab yi kira ga bangarorin biyu da su cigaba da rungumar juna domin tabbatar da an samu tsaro Mai inganci a jahar Zamfara. domin rashin tsaron na daya daga cikin manyan matsalolin da su ka hana Cigaban jahar Zamfara. Duk Inda matsalolin su ke a kawo rahoto ga mai martaba
Da ya ke jawabi Sarkin kiyawan Kaurar Namoda. Alh. Muhammad Ahmad Asha (MFR) ya yi godiya ga Al'ummar da su ka halarci wannan taro, haka Zalika ya yi kira, ga Al'ummar da su Marawa yunkurin gwamnatin jahar Zamfara baya, tare da Kira da a sauya jami'an tsaron 'yan Sada da su ka yi shekara biyar suna aiki a cikin karamar hukumar Kaurar Namoda.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
1st March, 2020

