GWAMNATIN ZAMFARA TA YI GAGARUMIN TARON SULHU TSAKANIN FULANI DA HAUSAWA A MASARAUTAR MARU - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 2 March 2020

GWAMNATIN ZAMFARA TA YI GAGARUMIN TARON SULHU TSAKANIN FULANI DA HAUSAWA A MASARAUTAR MARU


A cigaba da yunkurinta na ganin ta kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara. Karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun. Ta bullo da shirin sulhu a jahar Zamfara, Wanda shi ne silar shawo kan matsalar tsaron da ke addabar jahar.

Taron Wanda ya gudana a fadar Mai Martaba Banagan Maru  Alh. Abubakar Gado Maigari karkashin jagorancin Kwamishinan tsaro da ayukkan cikin gidan jahar, Hon. Abubakar Muhammad Dauran Justice, zaman Wanda ya kunshi dukkanin uwayen kasar Maru, sarakunan Fulani da ardo-ardo na masarautar. A lokacin taron an tattauna akan matsaloli jefi-jefi da ke fuskantar yankin da kuma yadda za a hada kai domin ganin an magance dukkan matsalolin da ke yankin. Daga karshe dukanin bangarorin sun yi jawabai masu ratsa zuciya tare da alkawarin cewa za su zama jakadun kirki wajen Samar da tsaro a jahar.

Da ya ke jawabi Kwamishinan tsaron ya nuna matukar jin dadinsa akan hadin kai da aka samu a tsakanin" bangarorin biyu, tare da yin Kira ga 'Yan uwa Fulani da Hausawa da su dawo da halin kirki da mutunci da aka sansu da shi. Ta hanyar zama lafiya da junansu. Daga karshe ya yi kira ga bangarorin biyu da su cigaba da rungumar juna domin tabbatar da an samu tsaro Mai inganci a jahar Zamfara. domin rashin tsaron na daya daga cikin manyan matsalolin da su ka hana Cigaban jahar Zamfara. Duk Inda matsalolin su ke a kawo rahoto ga mai martaba, Banagan Maru, kasancewar Sai da zaman lafiya ne, yankin zai samu cigaba

Da ya ke jawabi Banagan Maru. Alh. Abubakar Gado Maigari ya yi godiya ga Al'ummar da su ka halarci wannan taro, haka Zalika ya yi kira, ga Al'ummar da su Marawa yunkurin gwamnatin jahar Zamfara baya, domin kawo _

Abdulmalik Saidu Maibiredi

Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State

2nd  March, 2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here