A cigaba da yunkurinta na ganin ta kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamnan jahar Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun. Wanda tun bayan hawansa kan karagar mulki, a 29-5-2019 ya dauki aniyar kawo karshen matsalar tsaron jahar Wanda ya Kai shi ga bullo da shirin sulhu, Wanda shi ne ya kawo saukin matsalar tsaron da ke fuskantar jahar. Sai dai 'Yan matsaloli da ake samu nan da ke can wanda kullum ake fadi-tashi domin ganin an magance su. Kuma shi ne ya haifar da wannan zaman domin ganin an shawo kan matsalar sayar da shanun sata
Zaman Wanda ya gudana karkashin jagorancin Kwamishinan Ma'aikatar tsaro da Lamuran cikin Gida na jahar Hon. Abubakar Muhammad Dauran Justice. Zaman ya kunshi dukkanin sarakunan Zango na jahar Zamfara.
A yayin zaman dai an tattauna akan yadda sarakunan za su baiwa gwamnatin jahar, wajen ganin cewa an kawo karshen matsalar satar shanun da ke ake samu nan da can.
A jawabin Kwamishinan sarakunan Zangon su ne ke da muhimmiyar gudumawa da za su taka wajen ganin an magance matsalar satar shanu, kasancewar idan ba su yi hanya aka sayar ba to masu satar za su dena ne.
Musamman ganin cewa su ke sayar da shanu kuma duk wasu shanun sata da za a sayar to dole sai da saninsu. Don haka Kwamishinan ya baiwa sarakunan zango damar su tashi tsaye wajen aikinsu, domin ganin sun tsaftace aikinsu na sayar da shanu, domin muddun ba su bayar da gudunmawa ba, to za a wayi gari su kansu aikin nasu ya gagare su.
Daga karshe su kansu sarakunan zangon su bayyana cewa dukkaninsu za su bayar da gudumawa dari-bisa-dari domin ganin cewa duk wani burbushin satar shanu da sayar da shanun sata ya zama tarihi a jahar Zamfara.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State

