An samar da jihar Zamfara a shekarar 1996 zamanin mulkin Shugaba General Sani Abacha, jihohi shida aka samar ciki har da jihar Zamfara, Uku daga cikin jihohi shidan da aka samar dukkansu suna da Airport wanda hakan ke temakawa al'ummar jihar wajen tafiyar da ayyukansu na yau da kullum, kuma hakan ke bawa masu zuba jari damar ziyartar jihar a duk sanda suka bukaci zuwa jihohin...
Idan muka kalli jihohin Nassarawa da Gombe wadanda suke a yankin Arewacin Nigeria zamuga dukkansu sun samar da Airport din da mutanen jihar ke amfani dasu wajen hawa jirgi tare da sauke kayayyaki kai tsaye a cikin jiharsu, Mahajjatan jihar Gombe tun a shekarar 2018 suka fara hawa jirgi a cikin jiharsu maimakon yadda suke shafe doguwar tafiya a baya kafin suje Airport din da zaa kwashesu zuwa Kasar Saudia....
Maigirma Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya tsara zai samar da kayatacciyar Airport domin kara habaka tattalin arzikin al'ummar jihar Zamfara da kuma samar da tsaro ga manyan yan kasuwar duniya da suke da burin zuwa su saka jari a bangarori masu yawa a jihar, ko a cikin tafiyar da maigirma Gwamna yayi zuwa kasar China a kwanakin baya rashin Airport a jiharsa hakan yaso ya kawo matsala akan tattaunawar da sukayi da yan kasuwar kasar China da suke shirin zuba hannayen jari a jihar, sun tambayeshi Kilometers nawa ne daga Airport zuwa cikin Birnin Gusau, amma sai yake sanar dasu ai jirgi na sauka ne a jihar Sokoto sannan a hau mota a karaso zuwa cikin jihar, badon yan kasuwar sun aminta da amincin Maigirma Gwamna ba, da rashin Airport ya dakatar dasu daga zuwa su saka hannayen jari a jihar...
Koda a bangaren samar da ayyuka, gina sabuwar Airport zai temaka wajen samawa matasa aiki, tun daga lokacin gini har zuwa ga daruruwan matasan da zasu samu aiki bayan an kammala aikin, sannan hakan zai bude kofofin alherai ga jihar, sannan zai dora jihar akan tsarin tafiye tafiye ga masu yawan shakatawa na duniya....
Al'ummar jihar Zamfara kwarin gwiwa Gwamna Matawalle ke bukata don kara inganta jiharmu ta zamfara, anyi sa'ar dashi Gwamna burinsa ya gina jihar tare da al'umma ba wai ya kwashe dukiyarsu ba...

