YARI NA BARAZANA GA TSARON ZAMFARA!!! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 3 February 2020

YARI NA BARAZANA GA TSARON ZAMFARA!!!

#MAM

A wurin taron zaman jimami na Ƙarshen wata-wata da suke gudanarwa, tsohon gwaman ya yi waɗansu kalamai da suke zama na tunzura jama'a da kuma rainawa magoya bayan shi wayo. Sai dai kuma yan magana suna cewa "Idan maye ya mance to uwar da ba zata mance ba".

1. Daga cikin kalaman na shi ya bayyana cewa sun amincewa magoya bayan su da su kare kansu a duk lokacin da za a ci zarafin su, to sai dai kuma abun Tambaya a nan shi ne; shin wa ke cin zarafin magoya bayan
na su? Amsa anan ita ce; A tsarin mulkin Nigeria babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma duk wanda ya aikata laifi to jami'an tsaro ne keda alhakin damƙe shi da kuma miƙa shi gaban ƙuliya domin ya girbi abunda ya shuka. Dukkanin magoya bayan jam'iyar APC da hukuma ta cafke, babu ɗaya daga cikin su da mai daraja Gwamna Bello Matawalle ya bayar da umurnin a damke shi, jami'an tsaro ne da kansu suka ga girman laifukkan da suka aikata har suka gurfanar dasu gaban ƙuliya. don haka kalaman gwamna Yari na cewa idan aka zo cin zarafin magoya bayansu su kare kansu, to yana haɗa magoya bayan shi da jami'an tsaro ne, wanda hakan babban kuskure ne, matuƙar dai mutum ya aikata ba daidai ba to ya shiryama fuskantar hukuma.

2. Akan maganar da tsohon gwamnan ya yi na cewa Haƙƙin Al'umma ne aka ɗauka aka baiwa mai daraja gwamna Matawalle, ba zaɓen shi akayi ba'. Wannan maganar abun dariya ce, kuma suna cikin maganganun da tsohon gwamna Yari da magoya bayan sa ke yi a duk lokacin da 'Raɗaɗin ritayar su' ta motsa, idan hukuncin kotu zalunci ne, to gwamna Yari shi ne babban Azzalumi, kasancewar ya yi amfani da hukuncin "Black Market" na babbar kotun jaha wajen shiga babban zaɓen 2019 ta haramtacciyar hanya, kasancewar duniya ta shedi basu gudanar da zaɓen fitar da gwani ba (Primary Elections), don haka wannan zaluncin ne da ya ƙulla kotun daukaka ƙara dake Sokoto ta walwale kuma babbar kotun kolin Nigeria ta tabbatar da walwaler a ranar 24/05/2019. Don haka idan har akwai wanda ya zalunci Yari da magoya bayan shi to bakowa bane face shi kanshi Yarin da kanshi.

3. Akan maganar bin doka kuwa da Yari ya yi, wannan magana ta bamu mamaki matuƙa, kasancewar yan magana suna cewa" Mai ɗa a goye baya cewa ɗan wani shege". Sanin kowa ne a lokacin mulkin tsohon gwamna Yari babu wata doka da yake mutuntawa tun daga dokar majalisa har zuwa dokar kotu. Gwamnatin Mai Girma Gwamna Matawalle gwamnati ce dake bin doka da oda sau da kafa, kasancewar ta san muhimmancin doka. Da ace ba ta bin doka da oda to da bata ƙyale shuwagabannin ƙananan hukumomi da gwamnatin Yari ta ɗora gab da ƙarewar wa'adin mulkinta ba.

4. Tsohon gwamna Yari ya yi maganar rusa gidajen mutane da hukumar ZUREPB keyi. To ya kamata mu tuna mashi idan ya mance, hukumar ZUREPB hukuma ce ta dake da hurumin kula da yanda ake gina gidaje a duk faɗin jahar Zamfara, kuma ita ce keda Alhakin bayarda izinin yin gini a duk faɗin jahar Zamfara, duk wanda bai nemi izininta ba ko ya kaucewa tsarin gini da doka ta tanada to hukumar na da damar ɗaukar matakan da doka ta amince da su. Babu yanda za a yi mai girma gwamna Matawalle ya dawo yana baiwa hukumar ZUREPB umurni, kasancewar akwai shuwagabannin dake da alhakin kula da ita. Gwamna Matawalle jagora ne da ya baiwa ɗaukacin hukumomi da ma'aikatun jahar Zamfara yancin gudanar da ayukkan su da doka ta tanadar masu. Ba kamar a lokacin gwamnatin Yari ba da komai shi ke gudanar da shi.

5. Wani abun dariya da tsohon gwamna Yari ya faɗa cewa Wai su ne keda jami'an yan sanda da na gidajen yari. Sanin kowa ne waɗannan jami'an da Yari ke magana akan su, ma'aikata ne na gwamnatin tarayya masu bin doka da oda, ba wai ma'aikatan wata jam'iyar siyasa ba, don haka abun dariya ne wani mutum guda ya yi ikirarin su ne ke da waɗannan jami'ai. Duk wanda ya aikata laifi to alhakin waɗannan jami'an ne su gurfanar da shi a gaban ƙuliya. Don haka idan Yari na tunanin zai iya amfani da waɗannan jami'an wajen cimma manufar shi ta siyasa to yana zolayar kansa ne kawai.

6. Wata magana da ta ja hankalinmu a kalaman da Yari ya yi ita ce 'kiran kwamishinan yan sanda a matasayin shugaban tsaro na jahar Zamfara'. Tambayarmu ga Yari shin yaushe ya gyara kundin tsarin mulkin Nigeria ya mayar da kwamishinan yan sanda a matsayin shugaban tsaro na jaha? Sanin kowa ne gwamna shi ne shugaban tsaro na jahar shi, ba a Zamfara kadai ba har ma da daukacin jahohin Nigeria. Kuma shi kanshla yari a lokacin da yake yawon 'haramtaccen' yakin neman zaɓe a shekarar 2019 da ta gabata, duniya ta shedi yanda ya rinƙa yin barazana ga shugaban hukumar zaɓe ta kasa, farfesa Mahmud Yakubu da kuma shugaban jam'iyar su ta APC Adams Oshiomole, inda a lokacin ya rinƙa bayyana cewa 'Idan babu APCn Zamfara a cikin zaɓe to zaɓe ba zai yiyu ba a Zamfara, kasancewar shi ne 'shugaban tsaro' na jahar Zamfara.

Don haka yanzu abun dariya ne mu ji 'Ruɗaɗɗen' tsohon gwamna Yari yana kiran kwamishinan yan sanda a matsayin shugaban tsaro na jahar Zamfara. Ko tsohon gwamna Yari ya ƙi ko ya so, mai girma gwamna Matawalle shi ne shugaban tsaro na jahar Zamfara, kuma ba zai zura ido waɗansu tsiraru su tarwatsa 'zaman lafiyar' da aka samu a cikin jahar Zamfara ba, a matsayin shi na wanda Allah ya baiwa jagorancin Al'ummar jahar Zamfara.

Daga ƙarshe muna jan hankalin Al'ummar jahar Zamfara da su cigaba da goyawa gwamnatin mai girma Bello Matawalle baya a ƙoƙarin shi na dawo da jahar Zamfara akan turba madaidaiciya, da kuma gyara ɓarnar da gwamnatin 'kama karya' ta tsohon gwamna Yari tayi shekaru 8 tana tabkawa.

Haka zalika akwai buƙatar yan jam'iyar adawa ta APC su guji ɗaukar zugar da tsohon gwamna Yari keyi masu da waɗansu tsiraru dake zaune a Abuja, kada mutum ya bari ya faɗa tarkon jami'an tsaro, alhakin waɗanda suke tunzura su suna can Abuja kwancen su da iyalan su.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here