A cigaba da yunkurinta na ganin ta kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamnan jahar Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun. Wanda tun bayan hawansa kan karagar mulki, a 29-5-2019 ya dauki aniyar kawo karshen matsalar tsaron jahar Wanda ya Kai shi ga bullo da shirin sulhu, Wanda shi ne ya kawo saukin matsalar tsaron da ke fuskantar jahar. Sai dai 'Yan matsaloli da ake samu nan da can wanda kullum ake fadi-tashi domin ganin an magance su.
Hakan ya sa yau aka shiryawa dukkan limamin Jumu'a na jahar. Taron bita na yini daya, domin fadakar da su akan irin rawar da ya dace su taka wajen kawo karshen matsalar tsaron da su ke tusgowa a jahar, tare da gudunmawarsu wajen kawo karshen matsalolin tsaron da jahar Zamfara ke fuskanta..
A wannan taron Malamai sun gabatar mukalu da su ka shafi sha'anin tsaro da kuma hanyoyin da ya dace gwamnati ta bi domin shawo kan wannan matsalar. Da kuma irin gudumawar da su limaman za su bayar domin kawo karshen wannan matsalar
Da ya ke jawabi Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun Wanda Sakataren gwamnatinsa Hon. Bala Bello Maru ya wakilta ya yi godiya ga dukkanin malaman da su ka gabatar da Kasidu da kuma limamai da su ka baro garuruwansu, haka Zalika ya yi godiya da irin hadin kai da su ke bayarwa na goyon baya domin ganin an kawo karshen wannan matsalar ta tsaro ta hanyar sulhu.
Taron dai Wanda ya gudana Sakatariyar Jibirin Bala Yakubu. Wanda ma'aikatar Tsaro da lamurran Cikin gida, hadin Guiwa da kwamitin wa'azi da Gina Masallatan Jumu'a ta jahar Zamfara. Mai taken: MUHIMMANCIN TSARO WAJEN KYAUTATA SHARI'A. Su ka shirya ya gudana ne a karkashin jagorancin Kwamishinan Ma'aikatar tsaro da Lamuran cikin Gida Hon. Abubakar Muhammad Dauran Justice. Ya ke jawabi Kwamishinan ya bayyana cewa har yanzu tana kan bakanta domin ganin cewa shirin sulhu ya dore, tare da kira ga limaman da su tabbatar sun cigaba da goyon bayan gwamnati domin daurewar jahar Zamfara akan tafarkin cigaba. Tare da tashi tsaye wajen kira ga Al'umma muhimmancin zaman lafiya a tsakanin Al'umma.
Taron dai ya samu halartar Kakakin majalissar dokokin jahar Zamfara, uwayenmu Sarakunan Gusau, Kaura, Kwatarkwashi, Kwamishinan Watsa Labarai da Al'adu, Mai baiwa Gwamna shawara akan sha'anin Sulhu, da sauran manyan malamai a kowane lungu da sako na jahar Zamfara da su kansu malamai.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
5/3/2020
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Thursday, 5 March 2020
Home
Unlabelled
GWAMNATIN TA SHIRYA GAGGARUNMIN TARON WAYAR DA KAI GA LIMAMAI DOMIN KAWO KARSHEN MATSALAR TSARO.
GWAMNATIN TA SHIRYA GAGGARUNMIN TARON WAYAR DA KAI GA LIMAMAI DOMIN KAWO KARSHEN MATSALAR TSARO.
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

