KOKARIN GWAMNATIN GWAMNA MATAWALLE WAJEN BIYAN BASHIN JARABAWA - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 6 March 2020

KOKARIN GWAMNATIN GWAMNA MATAWALLE WAJEN BIYAN BASHIN JARABAWA


Bayan an biya sashen bashi na makuddan kudi, hukumar jarabawar gaba da firamare ta NECO ta saki sakamakon jarabawar daliban jihar Zamfara na shekara 2019 da 2018.

Bugu da kari, a watan da ya gabata an ba hukumar WAEC zunzurutun kudi har Naira miliyan dari (N100,000000) a matsayin somin-tabi akan kokarin biyan kudi fiye da jumlar Naira Biliyan Biyu da Rabi na NECO da WAEC su ke bi bashi. Ku duba irin wannan dimbin bashin da aka tara cikin shekara takwas.

A hakikanin gaskiya, idan mutum ya san irin dimbin bashin da ya rataya a wuyan gwamnati wanda gwamnatin Yari ta bari, to zai yi mamakin irin yadda Gwamna Bello Matawalle ya ke ci gaba da gudanar da gwamnati a cikin irin wannan hali kuma har ya aiwatar da ayyukan more rayuwa.

Idan har an samu wasu matsaloli da ba a rasa ba, to ya kamata a yi masa uzuri ganin irin jajircewar da ya ke yi wajen tsamo jihar Zamfara daga halin kuncin da ta samu kan ta dalilin mummunan mulkin shekara takwas da ya gabata.

Ibrahim Bello Zauma
SSA NEW MEDIA
6/3/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here