GWAMNATN ZAMFARA TA YI ZAMA NA MUSAMMAN DA 'YAN SA-KAI, NA YANKUNAN DA KE FAMA DA MATSALAR TSARO. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 9 March 2020

GWAMNATN ZAMFARA TA YI ZAMA NA MUSAMMAN DA 'YAN SA-KAI, NA YANKUNAN DA KE FAMA DA MATSALAR TSARO.








A cigaba da yunkurinta na ganin ta kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamnan jahar Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun. Wanda tun bayan hawansa kan karagar mulki, a 29-5-2019 ya dauki aniyar kawo karshen matsalar tsaron jahar Wanda ya Kai shi ga bullo da shirin sulhu, Wanda shi ne ya kawo saukin matsalar tsaron da ke fuskantar jahar. Sai dai 'Yan matsaloli da ake samu nan da can wanda kullum ake fadi-tashi domin ganin an magance su.

Hakan ya sa yau aka gayyato dukkan tsofaffin 'Yan sa-kai domin tattaunawa akan matsalolin tsaron da ke fuskantar yankunansu, domin ganin an shawo kan su.

A wannan taron tsofaffin Yan sa-kai sun gabatar jawabai akan halin da yankunansu su ke ciki da kuma Kira ga gwamnati da jami'an tsaro da su tashi tsaye wajen magance wadannan matsalolin da ke addabar yankunansu.

Da ya ke jawabi Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun Wanda Sakataren gwamnatinsa Hon. Bala Bello Maru ya wakilta ya yi godiya ga dukkanin tsofafin Yan sa-kai da su ka gabatar da jawabai da kuma jinjina masu da su ka baro garuruwansu, haka Zalika ya yi godiya da irin hadin kai da su ke bayarwa na goyon baya domin ganin an kawo karshen wannan matsalar ta tsaro ta hanyar sulhu.

Taron dai Wanda ya gudana Sakatariyar Jibirin Bala Yakubu. Ma'aikatar tsaro da ayukkan cikin gidan jahar ce karkashin jagorancin Kwamishinan Ma'aikatar Hon.  Abubakar Justice Dauran  Ya bayyana cewa har yanzu Gwamnati tana kan bakanta domin ganin cewa shirin sulhu ya dore, tare da kira ga 'Yan sa-kai da su tabbatar sun cigaba da goyon bayan gwamnati domin daurewar jahar Zamfara akan tafarkin cigaba.  Tare da tashi tsaye wajen kira ga Al'umma muhimmancin zaman lafiya a tsakanin Al'umma. Tare da Kira ga dukkanin jami'an tsaron jahar Zamfara da su Kara tashi tsaye domin ganin wannan matsalar ta zama tarihi.

A bangare daya wakilin Mai Daraja Gwamna kuma Sakataren gwamnatin jahar Hon. Bala Bello Maru ya baiwa Yan sa-kai tabbacin Gwamnatin jahar Zamfara tana cigaba da kokarin ganin ta magance wannan matsalar. Kuma za ta kara zage damtse domin yakar duk Wanda bai kaunar zaman lafiya.

Haka Zalika Kwamishinan Yan Sanda CP Usman Nagwaggo da kwamandan runduna ta daya ta jahar Zamfara dukkaninsu sun bayyana cewa za su Kara zage damtse Don ganin sun kara karfafa tsaron rayukka da dukiyoyin Al'ummar jahar Zamfara.

Daga karshe aka gayyato Malam Abubakar Sodangi Wanda ya yi wa'azi Mai ratsa zuciya akan muhimmancin zaman lafiya.

Taron dai ya samu halartar Kwamishinan Watsa Labarai da Al'adu, Hon. Sulaiman Anka da  sauran 'Yan sa-kai na kowane lungu da sako na da ke fama da matsalar tsaro a jahar Zamfara.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State

9/3/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here