GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA CETO BALARABE, DA AKA YI GARKUWA DA SHI DAGA KASAR NIGER! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 12 March 2020

GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA CETO BALARABE, DA AKA YI GARKUWA DA SHI DAGA KASAR NIGER!



A cigaba da yunkurin da gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ke yi na ganin Al'ummar jahar sun zauna lafiya. 
Wanda ya haifar da shirin sulhu tsakanin bangarorin biyu da ke fada da juna, Wanda tuni dai shirin ya samu gagaruman nasarori, Inda aka wayi gari 'Yan Bindigar da dama su ka mika wuya tare alkawarin tallafawa gwamnatin domin kawar da duk Wanda bai son jahar ta zauna lafiya. Wanda zuwa yau kauyukka da dama da su ka Kaura sun koma muhallinsu haka Zalika kasuwannin da aka rufe a baya yanzu an bude su, mutane da dama da aka yi garkuwa da su yanzu an yi nasarar karbo su duk a sanadiyar wannan sulhun Wanda kullum ake ta fadi tashi, don ganin duk inda matsala take an magance ta.
Kwatsam Sai ga labarin an shigo yankunan Zamfara da Sokoto da wani Matashin  Balarabe da Yan Bindiga su ka yi garkuwa da shi, daga kasar Niger. Wanda hakan ya zaburar da gwamnatin jahar Zamfara. Inda cikin ikon Allah da biyar diddigi tare da hadin kai daga tubabbun 'Yan Bindigar da su ka rungumi shirin sulhu. Kwamishinan tsaro da Lamuran cikin Gida na jahar Hon. Abubakar Muhammad Dauran Justice ya shiga har cikin dajin da aka yi garkuwa da Matashin Balaraben ya karbo shi, tare da kawo shi Shelkwatar Yan Sanda da ke Gusau da yammacin jiya Laraba.
Matashin Balaraben Mai Suna Didi kader Ibrahim Dan shekaru 19 ne Wanda ya fito daga garin Abalack na jahar Tahoua da ke kasar Niger, yana jin harsunan Larabci, Faransanci da kuma Hausa.
Da yake jawabi Mai Magana da yawon hukumar Yan Sanda ta jahar Zamfara Sp Muhammad Shehu, ya bayyana cewa Yanto wannan Matashin yana daya daga cikin nasarorin da shirin sulhu ya Samar a jahar, haka Zalika ya yi kira ga Al'umma jahar Zamfara da su cigaba da kai rahoton duk wasu abu ba su yarda da su ba, ga jami'an tsaro.
Haka Zalika shi kansa Matashin ya yi godiya ga gwamnatin jahar Zamfara musamman Kwamishinan tsaro da ya shiga daji Don kurrum ya karbo shi, haka Zalika ya yi godiya ga jami'an tsaron Nigeria.
Tuni dai gwamnatin jahar ta sa an duba lafiyarsa tare da Sanar da iyayensa daga kasar Niger domin su zo a damka masu shi.
*Abdulmalik Saidu Maibiredi*
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
12/3/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here