JAWABI GA MANEMA LABARAI NA JAHAR ZAMFARA DAGA KWAMISHINAN WATSA LABARAI, ALHAJI SULAIMAN TUNAU ANKA, KAN MATAKAN DA GWAMNATIN JAHAR TA DAUKA DOMIN SHIRIN KO-TA-KWANA KAN YADUWAR CUTAR CORONAVIRUS, A YAU JUMU'A 20TH MARIS 2020 - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 20 March 2020

JAWABI GA MANEMA LABARAI NA JAHAR ZAMFARA DAGA KWAMISHINAN WATSA LABARAI, ALHAJI SULAIMAN TUNAU ANKA, KAN MATAKAN DA GWAMNATIN JAHAR TA DAUKA DOMIN SHIRIN KO-TA-KWANA KAN YADUWAR CUTAR CORONAVIRUS, A YAU JUMU'A 20TH MARIS 2020

JAWABI GA MANEMA LABARAI NA JAHAR ZAMFARA DAGA KWAMISHINAN WATSA LABARAI, ALHAJI SULAIMAN TUNAU ANKA, KAN MATAKAN DA GWAMNATIN JAHAR TA DAUKA DOMIN SHIRIN KO-TA-KWANA KAN YADUWAR CUTAR CORONAVIRUS, A YAU JUMU'A 20TH MARIS  2020 

Barka da Rana 'Yan uwa manema Labarai,

Kamar yadda ku ka sani annobar cutar Coronavirus, ta zama wata annoba da ta karade duniya baki daya. Haka Zalika kowace Kasa na cigaba da fadi-tashi Dan ganin an magance ta. Wanda ko a kwanakin nan gwamnatin tarayya ta yi ta bullo da matakai domin dakile watsuwar wannan annoba da ke kisa babu kakkautawa. Wanda ya sa suke duk wani Taron cinkoson Jama'a.

2. Baya ga fama da matsalar Yan Bindiga da ke addabar gwamnonin arewa maso yamma, gwamnonin yankin sun yi taro a Kaduna ranar 18-3-2020 Inda su ka tattauna akan matsaloli da dama, cikinsu har da biyar hanyoyin da za su Hana yaduwar cutar Coronavirus a yankin

Wanda ya hada da; Rufe dukkanin makarantannin gwamnati da masu zaman kansu, Samar da kayayyakin yaki da wannan cuta Don haka ta yaduwa a tsakanin Aal'umma.

3. Akan Hakan ne ya sa Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya zama na musamman da masu ruwa da tsaki akan wannan sha'anin wadanda su ka hada da: Ma'aikatar ilimi, da ta ilimi mai Zurfi, da Ma'aikatar Kimiya da kere-kere. Domin su dauki dukkan matakin da ya dace domin dakile yaduwa wannan annoba ta Coronavirus, ta hanyar umurtar da a Rufe dukkanin makarantannin gwamnati da masu zaman kansu na kwanaki 30 daga ranar Litanin 23-3-2020 haka Zalika wannan umurnin ya shafi duk wani Gangamin Jama'a

4. Shuwagabannin gargajiya da na Addini su na Muhimmiyar rawar da A su iya takawa domin yakar wannan annoba Don haka gwamna na Kira gare su da su Marawa yunkurinta baya domin ganin cewa cutar ba shigo jahar ba. Domin mun ga yadda kasashen musulmi kamar kasar saudiya da Iran su ka Rufe har Masallatai da wuraren ibada Don kurrum gujewa yaduwar wannan cuta mai kisa.

5. Muna kira ga dukkanin Al'ummar jahar Zamfara, da su bi wannan umurni na gwamnati domin gujewa barkewar wannan annoba. Haka Zalika tana kira ga dukkanin 'Yan jaridu da 'masu tu'ammali da kafafen sadar da zumunta na zamani da su tashi tsaye wajen wayar da kan Al'umma akan illar wannan cuta. 

6. Tuni dai gwamnatin jahar Zamfara ta tanadi kayan aiki Don auna matafiya da su ka shigo daga makwabtan jahohinmu da na kowane lungu da sako na kasar nan, da yau zuwa wani mako  .

Fassara:

Abdulmalik Saidu Maibiredi

Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State

20/3/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here