A cigaba da yunkurin da gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ke yi na ganin Al'ummar jahar sun zauna lafiya.
Wanda ya haifar da shirin sulhu tsakanin bangarorin biyu da ke fada da juna, Wanda tuni dai shirin ya samu gagaruman nasarori, Inda aka wayi gari 'Yan Bindigar da dama su ka mika wuya tare alkawarin tallafawa gwamnatin domin kawar da duk Wanda bai son jahar ta zauna lafiya. Wanda zuwa yau kauyukka da dama da su ka Kaura sun koma muhallinsu haka Zalika kasuwannin da aka rufe a baya yanzu an bude su, mutane da dama da aka yi garkuwa da su yanzu an yi nasarar karbo su duk a sanadiyar wannan sulhun Wanda kullum ake ta fadi tashi, don ganin duk inda matsala take an magance ta.
haka Zalika yau gwamnatin ta yi nasarar karbo mutum 14 a hannun masu garkuwar, dukkanin wadannan da aka karbo din maza ne kuma an karbo su ne a dajin karamar hukumar Anka ta jahar Zamfara. Ciki wadanda aka yi nasarar karbowar har da uban kasar Wuya Umaru Usman. Mutanen sha hudu dai dukkaninsu sun fito ne daga karamar hukumar Anka guda 10 a garin Yar Tasha, guda 3 a garin wuya sai guda 1 a Kauyen Ruwan-Zabo.
Da ya ke jawabi Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara, ya nuna matukar jin dadinsa da wannan nasarar da gwamnatinsa ta ke cigaba da samu. Tare da bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tukuru domin ganin ta Kare rayukka da dukiyoyin Al'ummar jahar. Haka Zalika Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa Tana cigaba da aiki tukuru domin tabbatar da shirin ta na sulhu Wanda ya kai ga nasarar sakin wadannan mutane. Don haka wadanda su ka ki mika wuya gwamnatin za ta tabbatar ta daukar masu matakai domin ganin bayansu, kamar yadda ta Fara a yankin Magamin mai Tarko da wasu yankuna masu fama da wannan matsalar.
Haka Zalika su kansu wadanda aka ceto din sun nuna matukar jin dadinsu tare da godiya ga gwamnatin jahar akan wannan ni'imar da ta sanya su ciki. Tare da rokon Allah ya kawo zaman lafiya dauwamamme a jahar dama Najeriya baki.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
24/3/2020





