Hadaddiyar kungiyar kungiyoyin jahar masu ZAMAN kansu (ngos) sun mayarwa wata kungiya mai suna “Center for protection of right of citizens Zamfara state" Wadda ta yi Kira ga kotun koli ta gaggauta Yanke hukunci. Kuma ta baiwa APC bangaren tsohon gwamnan jahar Abdulazizu yari nasara. Tare da baiwa gwamnatin jahar wa’adin mako biyu ta saki ‘ya’yan APC da ta Kama.
Da ya ke jawabi shugaban Coalition of ngos na jahar zamfara Ibrahim TUDU ya nisanta kansu da wannan kungiya. Tare da Kira ga kotun ta yi adalci.
Haka zalika shugaban ya bayyana cewa Kwata-kwata wannan kungiya ba su san da ita a jahar zamfara ba. Haka zalika kungiyar ba ta taba yiwa jahar zamfara wani abin kirki ba. Hasalima babu sunan wannan kungiya a cikin jerin kungiyoyin jahar zamfara. Kuma ko takardar da su ka fitar babu lambar waya, ko sunan wani balantana ofishin kungiya ko wani abu da zai nuna ainahin kungiya ce ta yi wannan kiran.
Hasalima hadakar kungiyoyin sun bayyana cewa wannan taron manema labarai da wannan kungiya ta kira ya sabawa tsarin aikin kungiyoyi masu zaman kansu. kasancewar ba kungiyar da ke da tikitin shiggigi ga bangaren shari’a. Uwa uba baiwa kotu umurni. A bangare daya hadakar kungiyoyin sun bayyana cewa kiran da kungiyar ta yi na a sako wasu yayan jam’iyar APC all jahar ZAMFARA da ke gidan yari ya nuna cewa wasu ne daban su ka kira kansu da sunan wannan kungiyar.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
26/3/2020

