ZAMFARA ZA TA RUFE IYAKOKINTA SABODA ANNOBAR CORONAVIRUS - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 26 March 2020

ZAMFARA ZA TA RUFE IYAKOKINTA SABODA ANNOBAR CORONAVIRUS


Gwamnatin jahar ZAMFARA za ta rufe dukkan hanyoyin shiga da fita jahar daga jibi assabar har mako biyu.

Wannan umurni ya fito ne daga bakin mai daraja gwamnan jahar Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun . Gwamnan ya bayyana cewa kafin daukar matakin rufe dukkanin iyakokin sai da ya tattauna da takwarorinsa na jahohi makwabtal. Kuma rufewar ta mako biyu ta zama dole, la’akkari da sai da lafiya ne, al’umma za su ji dadin zurga-zurga.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa tuni ta yi shirin ko-TA-kwana, domin tabbatar da cewa al’umma jahar zamfara ba su kamu da Wannan annoba ba.

Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa zai rika zagayawa domin tallafawa al’umma. Tare da kira ga al’ummar jahar da su cigaba da baiwa gwamnatinsa goyon baya,tare da addu’ar samun nasara

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
26/3/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here