Gwamnan Jahar Zamfara Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya Kai ziyarar gani-da-ido, a iyakar Zamfara da Katsina. Gwamnan ya kai ziyarar NE, domin tabbatar bin dokar da ya kafa ta hana shiga ko fita Jahar Zamafara, Domin kariyar Al'ummar Jahar daga annobar Coronavirus.
A Lokacin ziyarar gwamnan ya zagaya Domin ganin yadda aikin Rufe iyakar ke gudana. Tare da yabawa jami'an tsaro da na kiyon lafiya da ke iyakar, tare da karfafa su, Domin tabbatar da sun yi aikinsu Kamar yadda ya dace.
Gwamnan ya cigaba da Bayyana cewa wannan rufewar iyakar ba ta shafi masu shigowa da kayan abinci da man fetur Ba. Don haka gwamnan ya yi kira ga dukkanin bangarorin da ke wannan aikin da su tabbatar sun yi aikinsu Kamar yadda ya dace, su kuma wadanda ke da dauke da kayan abinci ko manfetur a tabbatar an auna su kafin su shiga ko fita Jahar Zamfara. Domin kariyar rayukka da dukiyoyin Al'umma.
Haka zalika gwamnan ya Kara da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tukuru Domin kariyar lafiyar Al'ummarta.
*Abdulmalik Saidu Maibiredi*
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
30/3/2020

