Wani matashi daga Jahar Zamfara, Ya dauki nauyin zubawa 'Yan acaba 200 manfetur kyauta. Tare da masu KEKE NAPEP 100.
Matashin mai suna Abdallah Abeey ya Bayyana cewa ya dauki wannan matakin NE, Domin bayar da tashi gudunmawa wajen Samar da sauki cikin al'umma ganin yanayin da ake ciki da annobar Coronavirus ta mamaye duniya.
Matashin ya Kara da cewa daukar matakin na daga cikin biyayya ga gwamnan Jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, wanda ya yi kira ga sauran al'umma masu hannu da shuni Domin ganin talakawan Jahar sun samu sauki.
Haka zalika ya kara da kira ga dukkanin wadanda su ka amfana da wannan tallafin da su tashi tsaye wajen ganin sun yiwa al'umma sauki, a yayin ayukkansu Domin ganin cewa su kansu sun tallafa wajen kawowa al'umma sauki a cikin Jahar Zamfara.
Kowane Mai babur dai ya samu manfetur na Naira 1000 yayin da kowane mai NAPEP aka CIKA masa tankinsa.

