Shahararren Dan siyasar nan kuma Dan kasuwa a Jahar Zamfara Alh. Bashir Namada Ataka ya karkata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sadar da zumunta na zamani cewa ya raba gari da amininsa kuma tsohon gwamnan Jahar Zamfara Hon Dr Abdul'azizu Yari Mafara. Tare komawa jam'iyar PDP.
Ataka ya karyata jita-jitar ne Lokacin da ya ke tattaunawa da ya yi da Kafar maibiredi TV Kai tsaye.
Atakan ya Bayyana cewa har gobe yana tare da amininsa kuma maigidansa a cikin jam'iyar APC. Kuma ba wani labari mai kama da canza sheka da ya sani ko su ka yi magana da wani balantana maganar haduwar da aka ce sun yi da gwamnan Jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, na jam'iyar PDP.
Ya Kara da cewa wasu ne, su ka yi amfani da Damar da su ke da ita su ka sauya kan shugaba BUHARI a wani hoto da ya yi da Gwamna matawalle su ka ce ni ne.
Da Kafar mai maibiredi TV ta tambaye shi ko yana niyar sauya sheka, daga APC zuwa wata jam'iya ya Bayyana cewa; bai da wani shiri na yin hakan. Sai dai yana yiwa gwamnati mai ci a yanzu fatan Alheri. Musamman kudurinta na Samar da tsaron rayukka da dukiyoyin al'umma. Inda ya Bayyana cewa duk Wanda bai goyon bayan gwamnati ta wannan hauji to makiyi Zamfara ne.
Daga nan ya yi kira ga 'Yan siyasa da su tashi tsaye wajen taimakon matasa da raya kasa Domin cigaban Jahar Zamfara. Daga karshe ya yi kira ga masu yadda karya ko kazafi a kafafen sadar da zumunta da su ji tsoron Allah su dena.


