KWAMITIN KO-TA-KWANA KAN ANNOBAR CORONAVIRUS A ZAMFARA YA GANA DA MALAMAN ADDININ MUSULUNCI TARE DA RABA MASU KAYAN RIGA-KAFI.
A cigaba da yunkurinsa na yaki da tabbatar da annobar Coronavirus ba ta shigo jahar Zamfara ba. Kwamitin Ko-ta-kwana da gwamnatin jahar Zamfara ta kafa karkashin jagorancin Kakakin majalissar dokokin jahar Zamfara Rt hon Nasiru Mu'azu Magarya. A yau ya gana majalissar malamai ta jahar Zamfara karkashin jagorancin Malam Abubakar Aliyu Fari da tare limaman Jumu'a na jahar Zamfara, karkashin jagorancin Liman Dan Alhaji Sambo Gusau. Inda su ka tattauna akan hanyoyin da Malamai da limamai a jahar Zamfara za su tallafawa yunkurin gwamnatin jahar domin Kare rayukkan Al'umma daga annobar Coronavirus da ta mamaye duniya. Dukkanin bangarorin dai sun yi alkawarin marawa yunkurin gwamnatin jahar Zamfara baya domin ganin cewa ta ciki nasarar Kare al'ummarta daga wannan cuta.
Haka Zalika Kwamitin ya baiwa limaman masallatan Jumu'a manyan durorowan zuba ruwa domin wanke hannu kafin shiga kowane masallacin tare da sinadaran wanke hannu. Domin tabbatar da duk Wanda zai shiga masalatansu ya wanke hannunsa, kasancewar wanke hannu na daga cikin hanyoyin da masa kiyon lafiya su ka bayyana cewa yana taimakawa wajen dakile watsuwar wannan annoba.
A wata mai Kama da haka su kansu shuwagabannin kungiyar jami'an kiyon lafiya na jahar Zamfara sun kawowa Kwamitin gudunmawa ta sinadaran wanke hannu, domin bayar da ta su gudun, wajen hana wannan cuta shiga cikin Al'umma.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
14/4/2020
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Tuesday, 14 April 2020
Home
Unlabelled
KWAMITIN KO-TA-KWANA KAN ANNOBAR CORONAVIRUS A ZAMFARA YA GANA DA MALAMAN ADDININ MUSULUNCI TARE DA RABA MASU KAYAN RIGA-KAFI.
KWAMITIN KO-TA-KWANA KAN ANNOBAR CORONAVIRUS A ZAMFARA YA GANA DA MALAMAN ADDININ MUSULUNCI TARE DA RABA MASU KAYAN RIGA-KAFI.
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

