Duk da yanayin da duniya ta ke ciki na annobar Coronavirus, wanda ya sa al'amurran yau da kullum su ka tsaya cak!
Amma haka bai hana gwamnatin jahar fadi-tashi Don ganin ta tallafawa Al'ummar jahar ta hanyar da za su Dore cikin Walwala ba. Wanda hakan ne, ya sa Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya baiwa hukumar Fadama ||| kayan aiki domin tallafawa manoman rani da su ka hada da irin shinkafa, takin zamani, Injinin feshi, Maganin Kashe kwari da na Kashe haki, tare da takalmin shiga Fadama da safar hannu da kuma da kuma kayan sawa domin yin noman, da sauran kayayyakin aikin gona.
Hukumar Fadama ||| hukuma ce da take aikin hadin guiwa da Bankin duniya, Gwamnatin tarayya da jaha da kananan hukumomi in da su ke bayar da gudunmawa su kuma Manoma su bayar da wani kaso a ba su kayan aiki.
Sai dai shekaru da dama baya, shirin ya tsaya cak a jahar Zamfara. Saboda rashin bayar da kason da gwamnatin jahar Zamfara da ta gabata ba ta yi. Kasancewar Fadama ||| yana daga cikin sharuddan aikinta, dole gwamnatin jaha ta dauki nauyin Cigaba da aikin na wani lokaci kafin ta yarda ta dawo jaha, ta cigaba da aiki.
Hakan ya sa Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara ya warewa hukumar kudade domin sayen kayan aikin Rani ta baiwa kungiyoyin Manoman rani na kananan hukumomin Bakura, Mafara da Maradun domin su ne ke noman Rani a jahar Zamfara.
Da ya ke jawabi Jagoran shirin Fadama ||| na jahar Zamfara. ALH Sama'ila Abubakar Ribe. Ya bayyana godiya ga Gwamnatin jahar Zamfara akan fardado da wannan shirin, Wanda ya bayyana cewa Gwanman jahar ne, da kansa ya nuna sha'awarsa kan wannan shin, saboda amfaninsa ga Al'ummar jahar Zamfara da su ke mafi yawa Manoma. Dan haka yanzu kungiya goma ce kowace kungiya Tana da mutun goma-goma duk mutum dari su ne za suka amfana da wannan shiri yanzu. Kuma insha Allahu za mu tabbatar duk gudunmawa da ya dace mu bayar domin Cigaban Wannnan shiri mun bayar da ita.
Haka Zalika su kansu wadanda su ka amfana da wannan shirin karkashin jagorancin shugannsu na jaha, Alh. Isah Dankal sun nuna jin dadinsu da godiyarsu ga gwamnati, tare da alkawarin za su cigaba da marawa manufofin gwamnatin tare da amfani da tallafin da su ka samu ta hanyar da ta dace. Dukkan kungiyoyin dai sun bayar da kaso talatin cikin dari na kudin wadannan kaya da aka ba su, yayin da ita kuwa gwamnatin ta bayar da kashi saba'in.
Kaddamar da shirin dai ya gudana ne a sakatariyar karamar hukumar Talata Mafara. Wanda ya samu halartar Babban mai baiwa Gwamna Shawara akan sha'anin Noman Rani. Hon. Dan Yaro Abdullah, Babban Sakataren Ma'aikatar Gona da albarkatun Kasa a jahar Zamfara. Alh. Ibrahim Usman Dannabirgi Bakura. Wakilan kungiyoyin Manoman rani da muhimman mutane daga Fadama |||
*Abdulmalik Saidu Maibiredi*
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
15/4/2020
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
15/4/2020

