A cigaba da yunkurinta na yaki da annobar Coronavirus, Wanda rage cinkoson Jama'a na daga cikin matakai da ake dauka domin dakile wannan annoba.
Gwamnatin jahar Zamfara ta yiwa mutum 22 mazauna gidan yarin Gusau afuwa, wadanda aka yiwa afuwar da sun fito ne, ciki da wajen jahar Zamfara.
Da ya ke yawabi mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Wanda babban lauyan gwamnati, kuma Kwamishinan shari'a na jahar Zamfara. Barista Nura Zarumi Tsafe, ya wakilta, ya bayyana cewa, Gwamnan jahar Zamfara ya yi wa wadannan mutane afuwa ne, saboda laifukkansu kanana ne, don haka gwamna Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya yi masu afuwa, tare da ba su wani abin zaman gari domin su cigaba da rayuwarsu tare da kai wa ga iyalansu ganin wasu daga cikinsu sun fito ne daga jahohin Najeriya daban-daban wasu daga kudancin Najeriya.
Haka Zalika insha Allahu nan zuwa wani mako mai Daraja Gwamna zai sake yiwa wasu mutane masu kananan laifukka afuwa domin tabbatar da an rage cinkoson Jama'a a gidan yarin Gusau, Wanda yana daga cikin matakai da ake bi domin yakar annobar Coronavirus. Haka Zalika Kwamishinan ya yi kira ga wadanda aka yiwa afuwar da su zama mutanen kirki, tare da zama mutanen kirki a cikin Al'umma.
Wadanda aka yiwa afuwar sun nuna godiyarsu ga Allah gwamnatin jahar Zamfara tare da alkawarin zama mutanen kirki a cikin Al'umma.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
17/4/2020
17/4/2020

