KWAMISHINONIN JAHAR ZAMFARA SUN BAYAR TA TALLAFIN NAIRA MILIYAN 5 GA KWAMITIN KO-TA-KWANA KAN ANNOBAR CORONAVIRUS. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 17 April 2020

KWAMISHINONIN JAHAR ZAMFARA SUN BAYAR TA TALLAFIN NAIRA MILIYAN 5 GA KWAMITIN KO-TA-KWANA KAN ANNOBAR CORONAVIRUS.








A Cigaba karbar tallafi domin shirin KO-TA-KWANA kan annobar Coronavirus a jahar Zamfara,  Kungiyar Kwamishinonin jahar Zamfara karkashin Kwamishinan Shari'a,  Hon. Barista Nura Ibrahim Zarumi tare da Exco dinsa da ma'aji Ibrahim Jibo Magayakin Kaura. Da Pro Hon. Sulaiman Anka   da shugaban Kwamitin jin dadi da walwala Hon. Muhammad Maiturare, Bungudu. Sun ba da tallafin Naira Miliyan biyar ga Kwamitin KO-TA-KWANA kan annobar Coronavirus. Domin tallafawa Al'ummar jahar domin yakar annobar Coronavirus, da su ke bayar da tallafin Kwamishinonan sun bayyana cewa wannan na daga cikin gudunmawarsu ganin sun inganta Walwala da jin dadin Al'umma jahar Zamfara.
Da ya ke Mayar da jawabi shugaban Kwamitin KO-TA-KWANA kan annobar Coronavirus kuma Kakakin majalissar dokokin jahar Zamfara  Rt. Hon. Nasiru Mu'azu Magarya. Ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan tallafi da wadannan Kwamishinonin su ka bayar,  ya kuma yi alkawarin yin amfani da kudin domin tallafawa talakawan jahar Zamfara. Haka Zalika ya yi kira ga sauran masu hannu-da-shuninmu a jahar Zamfara da sauran Yan siyasa da su tashi tsaye wajen tallafawa talakawa.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
17/4/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here