GWAMNATIN ZAMFARA TA YI NASARAR KARBO MUTUM 12 HAR DA JARIRI A HANNUN MASU GARKUWA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 28 May 2020

GWAMNATIN ZAMFARA TA YI NASARAR KARBO MUTUM 12 HAR DA JARIRI A HANNUN MASU GARKUWA.











A cigaba da yunkurinta na ganin Al'ummar jaharta sun kwana da idonsu biyu gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun. Wanda hakan ne ya sa gwamnatin jahar ta bullo da shirin sulhu Wanda ya sa Al'ummar jahar Zamfara su ka samu Sauki matuka gaya ta fuskar tsaro. Tare da yin nasarar karbar daruruwan mutane a hannun masu garkuwa.

Wanda hakan ne ya sa yau aka samu Karin mutum 12 da gwamnatin ta karbo ta hanyar sulhun.

Da yake jawabi yayin Mika wadanda aka karbo din zuwa ga hukumar yansanda Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun Wanda Kwamishinan Ma'aikatar tsaro da Lamuran cikin Gida na jahar Hon. Abubakar Justice Dauran ya bayyana cewa wannan na daga cikin nasarar da gwamnatin jahar Zamfara ta samu tun bayan hawanta kan karagar mulki, Wanda ta bullo da shirin sulhu Wanda shi ne ya sa da dama daga cikin wadanda su ka karbi sulhun su ke ta fadi-tashi domin ganin cewa wadanda ba su karbi sulhu ba, sun karba, Wanda wadanda ba su karba su ke yakarsu tare da karbo wadanda su ka garkuwa da su, kamar yadda abin ya faru yau.

Haka Zalika shi kansa Kwamishinan Yan Sanda na jahar Zamfara CP Usman Nagwaggo, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jahar Zamfara akan gagarumar gudunmawa da hadin kai da take baiwa sha'anin tsaro. Tare da Kira ga su wadanda su ka yi sulhun da su cigaba Marawa yunkurin gwamnatin na kakkabe duk wani bata-gari da ke jahar.

Wadanda da yi nasarar sakowar sun hada da maza 9 mata 3 ciki har da jariri. Kuma mutanen sun fito ne daga garuruwan Sabon Birni 3, Yar Kirya 4  Dangulbi 1 Dankurmi 1 Kewaye 1 Sai Farar Kasa 2.
Abdulmalik Saidu Maibiredi 
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
28/5/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here