Da dama gwamnatoci kan fito da shiraruwan da manufar taimakawa Al'umma. Amma Sai shirin ya Kare kan wadanda ke da uwa a gindin murhu kurrum.
Hakan ya sa kungiyar Mai Mai aiki a Kasa da Kasa da ake Kira Save The Children ta gudanar da shirin jin bahasi ga kungiyoyin sa-sai da ma'aikatun gwamnati, da kuma kafafen Yada Labarai akan hanyoyin da su ke bi domin tabbatar da shiraruwan jinkai da gwamnatoci da kungiyoyin sa-kai ke yi.
Taron Wanda ya gudana a dakin taro na Taula Hotel &Apartments da ke unguwar Yarima Guwau. An tattauna akan matsalolin da dukkanin bangarorin ke ganin su ne ummil'aba'isin rashin nasara da kuma rashin taimakon Al'umma da ke faruwa a jahar Zamfara da kuma hanyoyin da za a bi domin magancesu tare da baiwa wadanda abin ya shafa shawara.

