A cigaba da yunkurinta na ganin Al'ummar jaharta sun kwana da idonsu biyu gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun. Wanda hakan ne ya sa gwamnatin jahar ta bullo da shirin sulhu Wanda ya sa Al'ummar jahar Zamfara su ka samu Sauki matuka gaya ta fuskar tsaro. Tare da yin nasarar karbar daruruwan mutane a hannun masu garkuwa. Sai dai wasu daga cikin Yan ta'addan har yanzu sun ki mika wuya tare da cigaba da cin karensu babu babbaka.
Wanda hakan ne gwamnatin ta dauki aniyar yakar duk wanda bai Mika wuya ba, ta hanyar mikawa jami'an tsaron wuka da nama domin fatatakar duk wani Dan bindiga da ya ki mika wuya Wanda tuni gwamnatin ta Samar da motocin sintiri tare jibge jami'an tsaro a wasu daga cikin dazukkan da wadannan Yan Bindiga ke cin karensu babu babbaka, Wanda hakan ya sa jiya aka samu karin mutum 22 da gwamnatin sojoji su ka karbo ta karfin maza, a hannun yan bindigar bayan sun yi garkuwa da su.
Da yake jawabi a yayin mika kubutattun mutanen ga gwamnatin jahar Zamfara, Jagoran rundunar Sojin jahar Zamfara OM Bello, ya bayyana irin gumurzun da su ka yi da 'Yan ta'addar kafin Kubutar da wadannan mutane.
Da yake jawabi yayin mika wadanda aka karbo din zuwa ga hukumar Gwamnatin jahar mai daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun Wanda Kwamishinan Ma'aikatar tsaro da Lamuran cikin Gida na jahar Hon. Abubakar Justice Dauran ya bayyana cewa wannan na daga cikin nasarar da gwamnatin jahar Zamfara ta samu tun bayan hawanta kan karagar mulki, Wanda ta bullo da shirin sulhu wanda ya sa aka yi nasarar karbo mutane da dama, baya ga wadannan da sojoji su ka karbo a jiya, bayan sun tarwatsa wadanda ba su karbi sulhun ba. Kwamishinan Ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jahar Zamfara akan gagarumar gudunmawa da hadin kai da take baiwa sha'anin tsaro. Tare da Kira ga su wadanda su ka yi sulhun da su cigaba Marawa yunkurin gwamnatin na kakkabe duk wani bata-gari da ke jahar. Tare da rokon Al'umma da su cigaba da Marawa yunkurin gwamnatin.
Da su ke jawabi wadanda aka ceto din sun bayyana matukar jin dadinsu tare da nuna matukar godiya ga wannan gwamnatin tare da rokon Allah ya cigaba da baiwa wannan gwamnatin ikon kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar jahar.
Wadanda da yi nasarar sakowar dukkanin su maza ne 22, 16 daga cikinsu sun fito ne daga jahar Sokoto yayin da 6 suka fito daga Zamfara 1 Anka, 1 Bukuyyum, sai 4 daga Bakura. Idan dai ba ku manta ba ko jiya jami'an Sojin sun yi nasarar kubutar da mutum 17 a hannun yan ta'addar.
Tuni dai gwamnatin bayar da umurnin a duba lafiyarsu tare da saya masu turu da abinci tare yin shirye-shiryen mika su ga iyalansu.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
State Coordinator Belmat Na Sallama
29/6/2020
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Monday, 29 June 2020
Home
Unlabelled
RUNDUNAR SOJI SUN YI NASARAR KUBUTAR DA MUTUM 22 A HANNUN YAN BINDIGA A ZAMFARA
RUNDUNAR SOJI SUN YI NASARAR KUBUTAR DA MUTUM 22 A HANNUN YAN BINDIGA A ZAMFARA
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.
