GWAMNAN ZAMFARA YA KADDAMAR DA BAIWA JAMI'AN TSARO MOTOCI 200 DON YAKAR MASU TAYAR DA KAYAR BAYA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 7 July 2020

GWAMNAN ZAMFARA YA KADDAMAR DA BAIWA JAMI'AN TSARO MOTOCI 200 DON YAKAR MASU TAYAR DA KAYAR BAYA.


A cigaba da yunkurinta na ganin ta kawo karshen matsalar tsaron jahar. Gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun.

Gwamnan dai ya kaddamar bayar da motocin ga dukkanin jami'an tsaron jahar Zamfara da su ka hada: 'Yan Sanda, sojojin Kasa da na sama, Dss da civil Defence, Hukumar Hana Shige da fice ta Kasa, Hukumar gyara Hali ta Kasa, da hukumar yaki Da cin hanci da rashawa, Da hukumar yaki da fataucin Miyagun kwayoyi Sai hukumar Hisba da kuma Zarota.

Da ya ke jawabi mai daraja gwamnan jahar Zamfara, Ya bayyana cewa raba wadannan motocin ya biyo bayan yunkurin Gwamnatinsa ne, na yaki da tada zaune tsaye a cikin jahar Zamfara.

Haka zalika Gwamnan ya yi kira ga dukkanin masu tayar da kayar da ba su aminta da sulhu da gwamnatin ba, da su yi gaugawar karbar shirin ba, in ba haka ba gwamnatin a shirye take domin yakarsu, da karfin tuwo kamar yadda ta Fara.

Da su ke jawabai shuwagabannin dukkanin rundunonin tsaron. Na jahar Zamfara sun bayyana godiya ga gwamnatin akan irin goyon bayan da gwamnatin ke ba su tare da alkawarin cigaba da aiki tukuru domin Kare rayukkan Al'ummar jahar da dukiyoyinsu. Tare da godiya ga Gwamnan akan Dawainiyar da yake yi da su.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
State Coordinator Belmat Na Sallama
7/7/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here