GWAMNAN ZAMFARA YA KADDAMAR DA BAIWA MABUKATA DARI TALLAFIN NAIRA DUBU HAMSIN-HAMSIN A HUKUMAR ZAKKA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 17 July 2020

GWAMNAN ZAMFARA YA KADDAMAR DA BAIWA MABUKATA DARI TALLAFIN NAIRA DUBU HAMSIN-HAMSIN A HUKUMAR ZAKKA.





A cigaba da yunkurinsa na ganin Al'ummarsa sun samu saukin rayuwa, Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, a jiya ya kadda da baiwa masu Dan karamin karfi tallafin Naira dubu hamsin-hamsin, har su Dari. Da ya ke jawabi wajen kaddamar da bayar da tallafin, Gwamnan na jahar Zamfara ya bayyana cewa daya daga cikin gurukkansa shi ne tallafawa masu Dan karamin karfi, domin bunkasa Walwala da jin dadinsu. Dan haka ya yi kira ga duk Wanda ya karbi tallafin da ya yi amfani da abin da ya samu Don ya dogara da kansa.

Da ya ke jawabi shugaban hukumar zakka da Wakafi na jahar Zamfara, Farfesa Kabir Umar Jabaka, ya bayyana matukar godiya ga irin gudumawa da goyon bayan da gwamnatin Barden Hausa ke ba su tare da bayyana cewa ita ce kashin bayan duk wani aikin tawali'u da hukumar ke yi.

Shirin bayar da tallafin dai ya gudana ne, shelkwatar hukumar da ke nan bye pass Gusau, ga mutum dari maza da mata, da ke da bukatu mabanbanta.

Shirin dai zai cigaba da gudana ne a duk watan Allah ta'ala Inda hukumar za ta rinka zakulo mutane dari-dari masu bukatu na musamman kamar, Bashi, rashin lafiya, kwarewa ko rushewar gida da sauran bukatu matara Kama da haka. Tana tallafa masu domin fitar da su daga cikin iftala'in da su ke ciki.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
State Coordinator Belmat Na Sallama
17/7/2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here