.
Marigayiyar ta kwashe kwanaki uku ana nemanta ruwa a jallo. Bayan ta fita daga gida a ranar talata 11-07-2017 da nufin zuwa bankin first bank da Ke Gusau, da domin buda asusun baki.
Malama Naja'atu Abubakar, an tsinci gawarta acikin gidan mijinta a wata shiyya ta musamman kuma a wani kebantaccen daki a yammacin ranar ta Jumu'a 14-07-2017.
Acikin dakin da anka tsinci gawarta an taradda cewa an fasa katangar dakin tare da haka ramen da za a bizne ta a bayan katangar dakin.
An taradda gawar Naja'atu Abubakar duk ta kunbura inda duk jikinta ya chanza siffa. Haka zalika an taradda gawarta daure da igiya tare da makkake gawar ta a tsakankanin wani tsani dake cikin dakin.
Tuni dai jami'an tsaro sun fara bincike domin gano musabbabin mutuwarta.
Kafin dauke gawarta daga gidan, mutane daga sassa daban daban acikin garin Gusau da kewaye su ke ta yin tururuwa domin ganarwa idon su tare da nuna alhinin su.
Koma miye sanadiyyar mutuwar Naja'atu Abubakar, bincike zai tabbatar.
Allah ya jikan ta da rahama ya baiwa iyalinta hankurin juriyar wannan babban rashi. Allahumma amin




