BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABA MUHAMMADU BUHARI, AKAN YUNKURINSA NA TAFIYA DA GWAMNAN JAHAR ZAMFARA, A KASAR AMERIKA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 16 September 2017

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABA MUHAMMADU BUHARI, AKAN YUNKURINSA NA TAFIYA DA GWAMNAN JAHAR ZAMFARA, A KASAR AMERIKA!

Tare da fatan kana cikin koshin lafiya, Mai girma shugaban kasarmu.

Allah ya kara maka lafiya da kwarin guiwar cigaba da jagorancin kasarmu kan adalci.

Mai girma shugaban kasa, muna tunanen Kasan halin da Jahar Zamfara take ciki. In kuma baka sani ba, to Bari mu Dan labarta maka.

Mai girma shugaban kasarmu, mun san kana bakin kokarinka na daidaita tattalin arzikin Najeriya, haka kana kokari matuka wajen baiwa jahohinmu hakkokinsu, a duk watan Allah ta'allah, Haka ka baiwa gwamnoninmu kudin London Paris club da na bailout, duk domin su samu damar biyan ma'aikata hakkokinsu, Ganin yadda mafiya yawan gwamnoninmu ke kokawa akan rashin kudin da su ke fama da shi. Wanda Gwamnanmu yana cikin gwamnonin da sunka amfana da wadannan kudade.

Alhamdulillahi,  Gwamnan ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA, Na Jahar Zamfara, na daya daga cikin gwamnonin da sunka amfana da wadannan kudade. Inda ya samu kudi zunzuruntunsu har Naira biliyan 37 da duriya.

Sai dai kash! Duk da wadannan makuddan kudaden da ka baiwa wannan Dan tahaliki, har yanzu bai iya biyan ma'aikatan Zamfarar mafi karancin albashi na dubu sha takwas (18,000) ba. Wanda shi ne Gwamna daya tilo a Najeriya da ya kasa aiwatar da wannan tsarin albashin. Haka zalika duk inda ka leka a ma'aikatun jahar zaka tarar da ma'aikata na cikin tashin hankali, ta hanyar kin biyansu hakkokinsu. Uwa uba uwayenmu, 'yan fensho, wadanda su ne, sunka bautawa kasarmu tun da kurciyarsu, Amma kwata-kwata ba maganar taimakawa rayuwarsu.

Wanda hakan ya haifar da shiga Yajin aikin da ya yi sanadiyar tsayar da komi cak! A Jahar Zamfara. Inda Assibitoci, Bankuna, Makarantanni da dukkanin ma'aikatun gwamnati sunka zama a rufe.

Wanda tun da anka Fara wannan yajin aikin, kwata-kwata Gwamnan kwashe inashi-inashi ya bar jahar. Dan ma kar ya ji ko ya ga halin da mu ke ciki 

Kwatsam! Sai munka tarar da labarin cewa, yana daya daga cikin gwamnonin da za su mara maka baya domin halartar taron Majalisar Dunkin duniya da za a yi a birnin NEW YORK, Na Amurika. 

KIRA!

Ya mai girma shugaban kasarmu, Hakika mun tabbatar da adili ka ke, kuma in ka ji wannan halin da mu ke ciki za ka tausaya muna matuka. Kuma na tabbatar da baka jin dadin halin da azzaluman gwamnonin Najeriya su ke sanya talakawansu ciki.

Dan haka, muna Kira gareka da Dan girman Allah ka soke wannan tafiyar da ka shirya da shi, tare da ba shi umurnin ya dawo ya shirya da talakawan da sunka zabe ku a tare.

Wanda muddun baka yi haka ba, ya mai girma shugaban kasa, wallahi mu talakawan Jahar zamfara. Baka kyauta muna ba, domin na tabbatar duk Wanda zai ga Gwamna Shehi kullum gaba-gaba a gun sha'anoninka zai dauka sak! Kai ya gado. Haka zalika zai dauka kana sane, ya Ke gasawa Zamfarawa aya a tafin hannu.

Dan Haka muna rokonka da ka taimaki rayuwar talakawan Jahar zamfara, ka yi baya-baya da Gwamna ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI ko zai sa shi taitayinsa.

Muna Rokon Allah ya sa wannan koke namu ya kai ga kunnuwan wadanda munka yi domin su. Ya kuma ba su ikon share muna hawayenmu.

Daga karshe muna rokon Allah ya fitar da mu daga cikin wannan mummun halin da mu ke ciki ya yi muna Mafita duniya da lahira.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Kasa Reshen Jahar Zamfara)

08069807496

16-9-2017

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here