Tun bayan kafuwar Gwamnatin a ranar 29-5-2011 zuwa yau. Ba ni tunanen akwai wasu gungun matasa da sunka amfana da wannan Gwamnatin, in ka debe wasu gungun matasa da mafiya yawansu sun taso cikin rashi kuma har yanzu su ke cikinsa. Wadanda sunka sadaukar da rayuwarsu wajen kafa gwamnatinsa Tun a 2011, yanzu kuma ya mai da su a cikin kwatocin garin Gusau. Suna CIGABA da yasarsu.
Tuni dai duk wata hanya da ake bi a taimaki matasan jahar da mai girma Tsohon Gwamna Alh. Ahmad Sani da wadda magadinsa ya dan dora, tuni wannan Gwamnatin ta kashe su.
Farawa da kashe duk wani bagire na koyar damu sana'o'in hannu domin mu dogara da kanmu. Tare da taimakon iyayenmu da 'yan uwanmu.
Maganar a taimaki rayuwar matasan jahar su nemi ilimi ba a maganarta, domin duk wani dalibin da ya kammala digirin farko NCE ko diploma bai taba amfana da naira da sunan tallafin gwamnatinsa ba.
Matasan da Gwamnatin ta isko suna kasuwanci tuni ta yi kutunguilar da za ta karya su, ta hanyar Daukar matakai iri daban-daban da zummar murkushe mu a cewarta wai yunkurin Samar da tsaro. Wanda hakan ya sa da dama daga cikinmu sun yi hijirar dole, mu da munka yi karfin Hali, garin na shirin fin karfin zamanmu.
Idan matashi ya yi karatu a jahar Zamfara, sai dai Ya Kalli Gwamnatin tarayya in yana son aikin Gwamnatin, in kuma Jahar zai KALLO! To fa da aiki. Domin tun da Gwamnatin ta hau kan karagar mulkin Jahar bata dauki matashi daya aiki ba. Wanda hakan kansa dole in mun turza mun yi karatun mu cigaba da zurawa takardun idanu, domin ba wajen Kai su!
Babbar masifar ita ce; Wallahi duk wanda Gwamna Shehi ZAI baiwa jahar a Matsayin Gwamna. Wallahi zai bar masa tarin matsaloli ne da sai ya Kai namijin gaske zai iya daidaita jahar.
Allah kai ne, ka halicci mu matasan jahar zamfara, kuma ka kebe wani nau'in na mulkinka ka baiwa wannan bawa naka!
Allah kai ne ka ce mu rokeka, kana karbar addu'ar bayinka. Allah ka karbi addu'armu, ka ceto mu daga cikin wannan mummunan yanayin da mu ke ciki.
Allah mun tuba!
Ya Allah ka albarkaci rayuwarmu ka zaba muna shuwagabanni masu tausayinmu a nan gaba!
Allah duk Shugaban da ba ya tausayinmu, Allah ka sansa, Allah mun rokeka ko kujerar KAMSILA kada ka ba shi. Allahumma amin.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
1-10-2017

