JAWABIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI A RANAR SAMUN ‘YANCIN KAN NAJERIYA SHEKARU HAMSIN DA BAKWAI - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 2 October 2017

JAWABIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI A RANAR SAMUN ‘YANCIN KAN NAJERIYA SHEKARU HAMSIN DA BAKWAI

1. Ya ‘yan uwa al’ummar najeriya, ranar daya ga watan oktoba rana ce ta musamman, irin ranar da dan Adam yake matukar farin cikin ganin irinta wato ta fita daga mulkin mu lukiya zuwa na ‘yancin fadin albarkacin bakinsa, wato mulki irin na dimokradiyya.

2. Ranar 1 ga watan oktoba dai takan kasance muhimmiyar rana da ke tuna mana irin kalubalen da kasar take fuskanta, a  don haka ta kan kasance ranar tuna baya da kuma godiya ga ubangiji da sake kara damarar fuskantar kalubalan da ke gabanmu.

3. ya kamata mu tuna da irin farin cikin da muke ciki na maido da mulkin dimokradiyya da irin abubuwanda suka faru tun daga 1999 zuwa 2015. A wadannan lokuta mun sami dama mai dimbin yawa, amma muka yi watsi da ita. A wadannan lokutan ne muke hako danyan mai ganga miliya biyu da rabi kuma ake sayar da kowace ganga a kan kudi kimanin dalar amruka dari.

4. A lokacin da jam’iyar APC ta nemi kuri’unku ta tabbatar muku cewa za ta share muku hawaye kan abubuwanda suke ci ma kasar tuwo a kwarya. Wadannan abubuwa kuwa sune dawo da tsaro, da daidaita tattalin arzikin kasa, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

5. Duk wadannan abubuwa ba abubuwa ba ne da muka fada da fatar baki, abubuwa ne da gwamnatin mu ta fuskance su ka’in da na’in wanda zamu iya cewa mun sami gagarumin nasara.

6. Cikin shekaru biyu da suka wuce Najeriya ta samu gagarumar nasara  ta fuskar harkokin siyasa domin a wannan lokacin ne gwamanti mai ci ta fadi zabuka cikinsu harda na ‘yan majalisar Tarayya, har ma da na Jaha. wanda wannan Ga ‘yan adawa zasu kalleshi a wani sabon shafin adalci ga siyasar kasa. Wanda ke nuna cewa muna dora siyasar kasar a kan kyakkyawan turbar dimokradiyya.

7. Wannan tagomashi ya biyo bayan irin ‘yancin fadan albarkacin baki da wannan gwammnati ta baiwa duk ‘yan Najeriya ba tare da tsangwama ba. Amma kuma wannan dama sai ta sanya wasu tsiraru suka yi amfani da ita wajen wargaza kan kasa da sunan sake fasalin kasa. Adon haka Wannan gwamnati ba za ta lamunta da duk wani abu da zai wargaza hadin kan kasa ba.

8. Na tuna lokacin da nake matashi a aikin soja, da ni akayi yakin basasa  mai cike da alhini na Biafara inda rai kimanin miliyan biyu ya salwanta da kuma salwantar da  dinbin dukiya ban da irin wahalar da yakin ya jefa dimbin ‘yan Najeriya. Na tabbata wadannan yaran masu neman kawo hargitsi a kasa ba a haife su ba a shekarar 1967 ballantana ma su san irin bala’in da aka shiga a lokacin.

9. Na yi matukar bakin ciki da yadda wasu daga cikin dattijan wannan yanki suka yi gum suka ka sa fadawa ‘ya’yansu gaskiya na illar abinda suke yi. Dattijan da sun ga irin abinda ya faru a wannan yakin.

10. Duk irin wanan fafutuka ya kamata ayi ta ta hanyar da ta dace bisa tsarin doka ta majalisunmu na tarayya da na jihohi amma ba ta amfani da wasu tsiraru masu son kawo fita a kasa ba.

11. Gwamanti tana tafiya bisa tsari wajen duba wannan al’amari da kuma duba koke koken ‘yan Naija Dalta domin magance abubuwan da suka dame su. A nan zan mika godiya ta ga shugabannin wannan yanki saboda hadin kai da suke baiwa gwamnati.

12. Game da sha’anin tsaro kuwa dole ne mu godewa sojojinmu wadanda suka jajirce wajen yakan ‘yan kungiyar Boko Haram da fatattakarsu daga wuraren da suka yi sansani wadanda yanzu suka koma irin yakin nan na matsorata na sari ka noke.

13. Najeriya tana godiya ga makwabtanta da kuma wasu kasashen duniya domin kawo karshen wannan bala’i na Boko Haram wanda irin yaki ne na ‘yan ta’adda da manyan kasashe na turai suke fama dashi.

14. Ba za mu gajiya ba har sai mun ga bayan guggun wadannan ‘yan ta’adda ta hanyar rundunar nan ta musamman ta Lafiya Dole.

15. Haka ma sojojinmu na sama su ma suna bayar da gudunmawarsu domin ganowa da kuma katse duk wasu hanyoyi da wadannan ‘yan ta’adda suke amfani dasu wajen gudanar da ta’addancinsu.

16. Har ila yau sojojinmu na ruwa su ma suna bayar da ta su gudunmawar ta kafa wani sansani a bakin tafkin chadi domin dakile ayyukan wadannan ‘yan ta’adda da kuma sake yaduwarsu.

17. Wanann gwamnati tana iyaka iyawarta wajen dawo da ‘yan matan nan na chibok da duk sauran mutanen da ‘yan Boko Haram suke garkuwa dasu.

18. Domin haka, muna kara marawa sojojinmu da kuma sauran jami’an tsaro baya da basu karfin gwiwa domin yaki da sace sacen mutane, da fashi da makami, da kuma rikicin nan na manoma da Fulani.

19. Game da tattalin arzikin kasa kuwa, wannan gwamnati ta sanya kaimi wajen tabbatar da cewa ta maida hankali sosai wajen harkokin noma domin kaucewa dogaro kacokan kan man fetur. Idan muka auna da makudan kudin da muka zuba na fiye da naira miliyan dubu 43 ta hanyar babban bankin Najeriya, wajen bayar da rance ga kananan manoma fiye da dubu dari biyu daga jihohi 29 na kasarnan wanda na kaddamar a a jahar kebbi a watan nuwambar 2015 wanda ya samu gagarumar nasara.

20.Wannan noma wanda aka yi shi a kadada murabba’in dubu dari biyu da talatin da ukku,
an sami nasarar noma kayan amfanin gona kala takwas da suka hada da shinkafa, da alkama, da masara, da auduga, da rogo, da waken soya, da kiwon kaji, da gyada, da kuma kiwon kifi.

21.Wannan aiki anyi shi ne tare da hadin gwiwar jihohi, Saboda haka ne ma nake mika godiya ta
ga gwamnoni kamar na jihar Kebbi, da Legas, da Ebonyi, da jihar Jigawa wajen noman shinkafa da  harkar rabon taki.

22.Haka nan ma bazan gushe ba sai na godewa gwamnonin jahohin Ondo, da Edo, da Delta,
Imo, da Cross Rivers, da Benue, da Ogun, da Kaduna da kuma jahar Filato wajen samun nasarar shiri na musamman na shugaban kasa a kan noman kwarar manja, da roba, da yazawa, rogo, dankalin turawa da sauran kayan amafnin gona.

23.Ruwan sama da Allah Ya albarkace mu da shi bara da kuma bana ya taimaka mana wajen samun amfanin gona mai yawan gaske.

24.Tun daga watan Disambar bara wannan gwamnati ta samar da taki buhu miliyan 7 ta hanun kamfanonin yin taki guda goma sha daya wadanda wannan gwamnati ta farfado dasu. wannan ya bamu dammar tsimin kudi dala miliyan dari da hamsin daga shigo da taki da kuma tsimin naira biliyan 60 wajen bayarda tallafin takin. Wanda kuma yasa farashin takin ya sauko daga Naira dubu 13 zuwa dubu 5 da 500.

25.Har ila yau, wannan hobbasa na shugaban kasa ya baiwa jihohi damar samar da ayyukan yi ga matasa dubu goma bisa tallafin shiri na musamman na babban bankin Najeriya.

26.Har ila yau, sha’anin wutar lantarki ya kasance babbar matsala amma gwamnati tana kara jari a wannan fannin domin magance matsalolin kudi da na ayyukan yau da kullum da ya dabaibaye wannan bangare domin samun wutar da za ta kai megawatt dubu goma a shekara ta 2020.

27. Muna fatan cimma wannan buri ne kuwa ta hanyar amfani da wuta daga hasken rana da kuma daga ruwa. A wannan gabace ma nake farin cikin farfado da aikin wuta na Mambila bayan shekaru masu yawa aikin yana tsaye cik.

28. Can a baya kuma wajen bangaren tattalin arzikin kasa, mun samar da yanayi mai kyau ga masu masana’antu, da masu zuba jari da kuma masu fitar da kayayyaki kasashen waje ta hanyar ba su kudaden chanji na kasashen waje.

29.Tun daga watan Afrilu, gwamnati ta samar da kudi ga wannan bangare day a kai Dala miliyan dubu 7. Wannan ya kara hankada tattalin arzikin kasa sama, kuma ya kara kwantar ma da masu zuba jari rai da ba su karfin gwiwa.

30. Watanni 7 da suka wuce sun tabbatar da samun daidaituwar hawa da sauka na kayayyaki. Naira tana samun daidaito daga Naira 525 a kan kowace Dala daga watan Fabarairu na wannan shekarar zuwa Naira 360 a yau.

31. Fadada hanyoyin tsare tsaren tattalin arzikin kasa yana ba mu dammar ficewa daga kiki kakan tattalin arzikin kasan da muka samu kanmu a ciki.

32. Har ila yau dai, domin a daidaita harkokin siyasa a kasa, gwamnati ta baiwa jihohi da kananan Hukumomi wasu basussuka daga kudin rarar mai da wasu hanyoyin kudade wadanda suka kai miliyan dubu dari 2 a shekarar 2015, da kuma naira miliyan dubu dari 4 da 41a shekara ta 2016 da kuma naira biliyan dubu daya a shekarar 2017 duk idan an hada kudin sun tashi fiye da naira biliyan dubu daya da naira miliyan dubu shida.

33. An dauki wannan mataki ne domin jihohin su sami damar biyan kwantan albashi, da ‘yan fansho da kuma kananan ‘yan kwangila wadanda aka kwantar shekaru da dama da suka wuce.

34. Karawa da karau, shirin gwamnati na naira miliyan dubu dari 5 domin ciyarda dalibai abincin da aka samar a gida, da bayarda rance ga masu kananan sana’o’i, da tallafawa tsofaffi da gajiyayyu, da kuma shirin samar da gidaje masu rahusa na cikin abubuwan da gwamnati ta baiwa fifiko.

35. Ya ‘yan uwa ‘yan Najeriya, na san cewa yaki da cin hanci da rashawa ba zai zamo da sauki ba. Mun san duk masu irin wadannan halaye zasu bi ko wace hanya domin tare yunkurin mu ta hanyar amfani da alkalai da kuma anfani da hanyoyin siyasa. Amma wannan ba zai sa guiwoyin mu su yi sanyi ba. Domin haka gwamnati ta baiwa kwararrun lauyoyinmu umurni da su tattara bayanai da kuma dawo da kayayyakin sata.

36. Wasu daga cikin hanyoyin da wannan gwamanti take amfani da su sun hada da amfani da tsarin tara kudaden a akushi daya, da ‘yan kwarmato, da sabon tsarin biyan albashi ta hanyar zamani.

37. Mun rattaba hannu akan wasu yarjeniyoyi da wasu kasashe akan munanan ayyuka kuma muna ganin haske daga bangaren shari’a. kwanan nan Babban mai Shara’a na kasa ya umurci alkalai da su gaggauta kammala shari’un cin hanci da rashawa kuma a hukunta duk wani mai shara’a da aka samu da karban na goro.

38. Kwanan nan ne aka nada toshon mai shara’a Salami domin ya kula da wadannan kotuna na musamman. Gwamanti tana matukar neman hadin kan wannan kwamiti.

39. Ina yabama majalisun dokokin tarayya domin kara tsara kwamitoci masu sa ido akan ayyukan ma’aikatun gwamnati. Kuma ya kamata su rika gaggauta  duk wata doka da ta shafi cin hanci da rashawa da aka kawo gabansu. Cin hanci da rashawa wani abu ne wanda duk ‘yan Najeriya sai sun tallafa domin a cimma nasarar yakarsa,ta hanyar kai rahoton duk wanda kuka kama da irin wannan halayya.

40. Ita kuma gwamnati a nata bangaren, za ta tabbatar da cewa tana tsantseni wajen tafiyar da arzikin kasa a matakan gwamantin tarayya, da ta jaha, da kuma ta kananan hukumomi.

41. A yayinda muka cimma rabin wa’adinmu , za mu kara zabura wajen kawo ci gaba da kuma daidaita dukkan al’amurran dake neman gyara.

42. Na gode kuma ina yi muku fatan ayi hutu lafiya. Alla Ya albarkaci kasarmu.
.
Fassarar kalaman Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gabatar yau kan cikar Nigeria hamsin da bakwai , da fatan Allah ya kara masa lafiya,kariya,imani,adalci tare da bashi ikon kammala ayyukan alkhairi da yake yiwa alummar wannan kasa.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here