KUNGIYAR HAFYDOF ZATA KARRAMA MARIGAYI SIR. AHMADU BELLO SARDAUNA DA MALAM IBRAHIM WAKKALA, DA WASU FITATTUN MUTANE - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 16 September 2017

KUNGIYAR HAFYDOF ZATA KARRAMA MARIGAYI SIR. AHMADU BELLO SARDAUNA DA MALAM IBRAHIM WAKKALA, DA WASU FITATTUN MUTANE


Kungiyar mai Suna Hausa/Fulani Youth Development and Orientation Forum (Hafydof) ta bakin jagoranta na kasa Comrade Abdul'aziz Tibibi. Ta bayyana cewa; "Kungiyar zata karrama mutane ne kamar haka;

"Sir Ahmadu Bello Sardauna of Sokkoto. Ta hannun Jikansa Alh Hassan Marafa (Magajin Garin Sokkoto) saboda gudunmawar da firimiyan arewar ya bayar ga cigaban AREWA lokacin da yana raye.

"Sai Kuma Mallam Ibrahim Wakkala Muhammad liman (Sarkin Malam Zamfara) Deputy Governor of Zamfara. Wanda kungiyar zata karrama saboda kokarinsa na sasantawa tsakanin makiyaya da Manoma abinda ya addabi Al'ummar karkarar jahar Zamfara, a shekarun baya. Wanda saboda wannan sasanci ne, ya sa anka samu manoma na noma a wannan shekarar.

" Haka zalika kungiyar zata karrama Hon Muhammad Gudaji Kazaure. Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi. Saboda kokarinsa na Yin wakilci mai inganci tare da Hulda da Al'ummarsa kamar yadda ya dace.

"Sauran wadanda za a karrama sun hada da; Eng. Muhammad Bello (Sarkin Narkuta), Ameenu Abubakar Ladan (Alan Waka) Dan kuma Ibraheem Sulaiman Dan Iro da tawagar sa (HAFYDOF Music and Entertainment Directorate) da kuma Jahohi karkashin kungiyar da za'aba Kambun TOP Three Team Award.


Comrade Tibibi ya cigaba da cewa "Lambar dukkanin wadannan mutanen da za mu karrama fitattu ne a arewa da kuma sun bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kawo sauyi a rayuwarsu tare da bautawa Al'ummar da ke zagaye da su. Kuma Insha Allahu Za'a bada wannan kambu ne a ranar Assabar 30-9- 2017 A Arewa House Kaduna. Domin tuni mun Sanar da dukkanin kungiyoyin matasan Arewa da sauran kungiyoyin da ke da'awar kawo sauyi a arewa."

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here