BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNA A.A YARI AKAN MATSALAR RASHIN SAKO SAKKAMAKON JARABAWAR WAEC DA NECO TA 2017 A JAHAR ZAMFARA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 13 October 2017

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNA A.A YARI AKAN MATSALAR RASHIN SAKO SAKKAMAKON JARABAWAR WAEC DA NECO TA 2017 A JAHAR ZAMFARA!

Assalamu alaikum! Hon. Alh.Abdul'azuzi Abubakar Yari Mafara. Bayan sallama irin ta addinin Musulunci, tare da fatan kana cikin koshin lafiya.

Ya mai girma gwamnan Jahata ta zamfara. Kamar yadda kusan kullum muke ta faman kiraye-kiraye, Musanman akan matsalar bangaren ilimin jahar zamfara. yau ma kamar kullum kai tsaye kira nake son in cigaba da yi duk dai, kan matsalar rashin sako sakamakon jarabawar WAEC da NECO a jahar zamfara!

Kasancewar nan dai ne kafa daya tilo da zamu iya yin kira, ya fada kunnuwanka.
Fatanmu ka natsu, domin hankaltowa, ka kuma sharema talakkawan jahata, hawayensu.

Zan so mai girma jagoran zamfarawa kayi tuni da cewa; duk dunbin dukiyar da ke hannunka a halin yanzu mallakar talakkawan zamfara ce, alfanunta a hannunka ka amfanar da zamfarawa da ita ta hanyar da; zasu ginu akan turba ta gari.
To abin tambayar a wane fanni ne yafi kyautatowa ka fi maida hankali dan ganin cewa dukiyar zamfarawa ta amfani zamfarawan???

Duk mai hangen nesa zai iya cewa; ba wani fanni da yafi dacewa, ka maida hankali a kansa kamar fannin cigaban ILIMIN ZAMFARAWA, wanda masana harshe ke kira da "gishirin zaman duniya".

Ai ko in haka ne ina ganin bai dace ka dauki matsayar mai da wannan fannin kurar-baya ba. Kasancewar tun da Allah ya damka maka jagorancinmu, munga take-takenka akan hakan.

La'akkari da na yi cewa "idan dambu yayi yawa baya jin mai" kuma wannan dan takaitaccen feji ba zai isa, in zayyano dukkan matsalolin da fannin ILMIN jahar Zamfara ke fuskatan ba.

Dan haka yau kai tsaye ina magane akan Dalibban da a kowace shekara suke zana jarabawar kare babbar makarantar Sikandire, amma kafin sakamakon tasu ya fito sai an kai ruwa rana, rayukkan dalibban sun kai matuka wajen baci, saboda da zaman jira.

Kamar kowace shekara, wanda yanzu  haka Tun ranar 18-8-2017  anka sako Sakamakon Jarabawar WAEC ga NECO a makarantanni masu zaman kansu, da ta sauran jahohin da sunka dauki ilimin Al'ummar jahohinsu da muhimmanci.

Amma su 'ya'yan masu gida a tsakar rana har yanzu suna nan su na zaman jiran gawon shanu. Duk da cewa a rana daya ne ake rubuta jarabawar tsakanin makarantanni masu zaman kansu da na gwamnatin.

Alhamdulillahi Duk dai uzurin da ya dace mu yima yi maka, ya mai girma Gwamnanmu wallahi, Allah shi ne shedu munyi, domin mu ga iya gudun ruwanka, ko da zaka dauki matakin biyan kudin wanda zai sa hukumar shirya jarabawowin su sako jarabawoyin, Amma Ina.

Yanzu ga shi an wayi gari; manyan makarantanni da dama a ciki da wajen jahar nan tamu sun fara jarabawar share fagen shiga, makarantannin. Mafiya yawan jami'o'in Jahohi da na tarayya sun kammala Jarabawowin daukar dalibbai na 2017/2018, Wanda baki daya ba talakan Zamfara daya da ya samu wannan damar.

Babban abunda ya kara tayar muna da hankali bai wuce ganin cewa damar da 'ya'yan talakkawan jahar Zamfara suke da ita tana kokarin kubuce masu ba.

Domin dai damar dan talakka a jahar zamfara ita ce ya nemi gurbin karo ilmi a COE MARU kasancewar ita ce makaranta mai dan sauki-saukin yi ga 'ya'yan talakkawa. To amma a shekararu uku da Sunka shude ni kaina sai da na zubar da hawaye. Domin kashi sitin na dalibban da Sunka samu gurbin karatu a Kwalejin, wallahi baki ne daga makwabtan jahohi.

Wanda yanzu haka mafiya dalibban da ke karatu a manyan makarantaninmu na jahar zamfara,  ba zamfarawa ba ne. Tabbas wannan babban abun kunya ne, har  azo cikin gidanka a fimu taka rawa!

Wannan kenan! Yanzu kuma ga wata shekarar ta dawo ba a biya kudaden ba Kuma ba mu san ranar biyan ba.....

Ya mai girma shugabana, shugabanmu ya kamata ka kula da cewa har yanzu uwayen yara da yaran suna kallonka su ga ya za ka yi da su da 'ya'yan na su. Domin ragama na hannunka, amma duk da haka har yanzu ba wani motsi da 'ya'yan talakkawa sun ka ga gwamnatinka nayi dan ganin cewa; gwamnatinka ta biya wadannan kudade domin suma 'ya'yan talakawan su samu damar zurfafa karatunsu. Kasancewar dukkan mutun mai kishin kansa, to fa yana son ya zama mai amfani ga kansa, danginsa, da Al'ummarsa ba ki daya. Dan haka hanya daya tilo da zai bi ya cimma wannan kuduri shi ne; ya tashi ya nemi ilmin domin shi ne zai yada masa hanya ya hango mafita.

Yadda Allah ya halitto mu, muna kara gode masa, mu talakkawa ne, kuma muna godiya ga Allah da ya sa kowa a mutun, mutane asshi. Dan haka kai kanka, da bazarmu kake taka rawa. Duk dai yanzu za ka iya cewa; "ka ci moriyar ganga ne, shi ya sa ka jefar da korenta"  to indai makidin kalagunne ba ranar da zai tuba da dukan ganga, haka za a wayi gari ka dauko ta har kaso ta yi maka zaki, wanda na tabbatar a ranar zakinta ba zai kwashi 'yan kallo ba.

Shawararmu dai har gobe a gareka ita ce; ka yi gaugawar debo kudi a asusun jaha, kasancewar ba wai kudin wasu mutane ne daban ba. A'a kudin al'ummar da kake jagoranta ne. Domin amfaninsu, gare su, shi ne; ka biya masu bukatunsu.

Daga karshe muke rokon Allah ya sa kiranmu ya isa a kunnuwanka, kai kuma ka amsa kiranmu, ta hanyar biyan kudin cikin lokaci. Su kuma dalibban muna yima su fatan Allah ya datar da su da sakkamako nagari, ya basu ikon wucewa su zurfafa karatun nasu. Ya Allah ka sa karatun nasu ya amfani al'ummar zamfara, Najeriya, da rayuwarsu baki daya.

Abdulmalik Saidu mai biredi tashar bagu, Gusau(Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here