KUTUNGUILAR GWAMNA EL-RUFA'I NA JAHAR KADUNA KO GYARA KAN 'YAN UWA MALAMAN PRIMARY JAHAR - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 14 October 2017

KUTUNGUILAR GWAMNA EL-RUFA'I NA JAHAR KADUNA KO GYARA KAN 'YAN UWA MALAMAN PRIMARY JAHAR

Duk Mai hankali, dole ya yi mamaki, a ce malamin Primary, ya kasa cin jarabawar dalibbai 'yan aji hudu na Primary.

Wanda tun a lokacin da rahoton ya fito cewa, Akalla sama da Malami dubu 20 ne, sunka kasa cin Jarabawar da anka yi masu ta 'yan firamare 4.


Sai dai a Jiya jumu'a 13-10-2017 mun saurari shirin ra'ayi Riga a bbc hausa da sunka yi kacokan¡ kan wannan balahirar. Wanda Alhamdulilahi an gayyato shi Sakataren kwamitin da shi KAKAKIN Gwamnatin Jahar ta Kaduna Wato Samuel Aruwa.

Inda Kai tsaye shi Sakataren kwamitin ya karyata Samuel Aruwa. Cewa su ba su ma fitar da sakamakon Jarabawar ma ba. Balantana wani ya ce ga wadanda sunka ci ko wadanda sunka fadi

HAKA zalika Sakataren ya ce Kashi saba'in da wani abu ne sunka ci JARABAWAR. Unlike yadda Gwamnatin ta ce.


Abun mamakin nan shi ne, Ina ganin in dai tsari Gwamnatin Jahar Kaduna ta ke son yi domin inganta harkar ilimi, kamata ya yi ta tabbatar ta yi Binciken kwakkwara dan debe malaman bugi, su kuma wadanda anka tabbatar sun yi karatun a tura su kwasakwasai Dan su kara gogewa. Wannan kenan!

Dan Haka Shawarata ga ita kungiyar malamai ta Jahar Kaduna da kungiyar KWADAGON JAHAR, su tabbatar su yi tsaye cewa ba a Kori wadannan 'ya'ya nasu ba.

A madadin haka su tabbatar an yi Binciken kwakkwara ga duk malamin da bai yi karatu ba a Kore shi, Dan bai iya karantarwar. Wadanda sunka yi karatun kuma a dauki matakin na kara ba su horon da za su kara kwarewa ta hanyar dabaru da hanyoyin koyarwa na zamani ta yadda za su koyar da dalibbai kamar yadda ya dace.


Wanda muddun anka yi haka za a samu sa'ida amma maganar kora ba ta ma taso ba.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
08069807196


14-10-2017

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here