BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR GUSAU, AKAN YINKURINSA NA MURKUSHE MASU KANANAN SANA'O'I. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 13 November 2017

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR GUSAU, AKAN YINKURINSA NA MURKUSHE MASU KANANAN SANA'O'I.




Assalamu alaikum, bayan Farawa da yi maka sallama Irinta addinin da munka yi tarayya da kai wato Musulunci.

Zan so wannan wasika ta riske ka cikin koshin, da nishadi (Ni Dai Wallahi cikin wani Yanayi na bakin ciki da damuwa na rubutu maka ita).

Bayan Haka zan so ka Dan natsu ka karanta wannan wasika da na ke da yakinin za ta riskeka.

Allah ya arzurta da arziki na kudi da mulki Farawa da kansila zango biyu a gundumarmu ta GALADIMA. Bayan ka kammala Allah ya yi maka sha Tara da arzikin zama mataimakin shugaban karamar hukumar Gusau, Allah mai yin yada ya so ya karbi rayuwar shugaban da Kake mataimakinsa (Allah ya jikansa da rahama ya sa ya huta ya sa aljanna firdausi ce a makomarsa). Ka haye Kan karagar mulkin Gusau Kamar yadda doka ta tanada, Haka zalika ka koma Kan kujerar bayan Zabe, Wanda yanzu Haka kai ne ke jagorantarmu cikin iyawar Allah. Kuma kana da gudurin neman Wata kujera a 2019

Na tabbatar da Allah ya yi maka gatan da in ka so za ka iya gode masa, tare da taimakon na kasa da kai.

Sai Dai kash! Shekaruna cikon cokali ne, Dan haka Wallahi ban taba ji ko ganin wani shugaban karamar hukumar da ya tsani mai karamar Sana'a tare da kokarin shafe su, Kamar kai ba. Hujja ta farko a nan ita ce;

Da hawa Kan karagar mulkinka ka sa anka Kori duk wani mai sana'a saman baro a kasuwar dare da ke Gusau. A lokacin da dama daga cikin wadanda ka kora daga inda sunka dogara shekara da shekaru, wasu sunka bar jahar, wadanda zaman jahar ya zamar masu dolen-dole sun tsaya amma mafiya yawansu sun Kare, a wahalce su ke ciyar da iyalinsu a yanzu.

Haka zalika ranar larabar da ta wuce 8-11-2017 ka Bada umurnin masu neman abinci a kasuwar jari-bola da su kwashe inasu-inasu, subar gun ba tare da La'akkari da irin halin da daruruwan matasa da dattijan da ke cin abinci wurin ba.

Kwatsam! Yau munka wayi gari da ganin wasu mutane. Da littafansu (a babbar Tashar motar Gusau), wai haraji za Su karba  Naira dubu-dubu  ga duk wani mai sana'a Kan teburi. Duk wanda bai bayar ba, sun tabbatar muna da MARECE za a KWASHE masa TEBURA.

Shi kuma Wanda bai fito ba akan dauke teburinsa daga inda ya aje shi (ba Mu San abunda hakan ke nufi ba. Kamar yadda munka ga an yiwa wani abokin sana'armu YUSUF SHU'AIBU GUSAU)

Wanda duk kai tsaye sunka tabbatar muna da cewa kai ne ka sanya su.

Wanda a halin da ake ciki yanzu, muddun shugaba ba son ya ke yi talawansa su shiga wani mawuyacin Hali ba. Wallahi dole ya taimaka masu. In kuma bai taimaka masu ba. To bai kamata ya nemi naira gunsu. Ganin cewa rayuwa, ta matukar tsananta ga talakawan.

Baka tallafawa 'yan kasuwa da jarin Naira ba,

Baka taba yi masu hanyar da za su samu ko da bashi domin inganta kasuwancinsu ba.

Baka taba jawo Wata kungiya domin tallatawa masu Kananan SANA'O'I dabarun kasuwanci ba.

A iya sani na ban taba ganin ka shi tasha ko kasuwa ka yi masu aikin naira da dukiyarsu.

Dan Allah ya kake son mu yi?

Sata?

Mola?

Ko mu bar jahar?

Amsa Wallahi ba za mu daya ba, kuma Wallahi sai mun rayu yadda ake ke so,  Wallahi sai mun yi karatu daukaka hannun Allah din ta ke!

SHAWARA!

Allah ya kai Kai ka wannan matsayi ba Dan ka ba shi naira ko ya fi kaunarka ba. Dan Allah ka yi kokarin yin ababen kirkin da ko bayan baka za mu ce Allah ya saka maka da ALHERI.

Daga muna rokon Allah ya rika ma talakawan jahar Zamfara da Najeriya kwata. Mai son takura masu kai ka sansa Allah ka shirya shi. In baya da rabon shiryuwa ka raba mu dashi.

Daga, Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau ( Sakataren kungiyar Masu Biredi ta Jahar Zamfara)

08069807496

13-11-2017

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here