DOKAR HANA MAKIYAYA YAWON KIYO A JAHAR BENUE KO TAUYE HAƘƘIN MAKIYAYA DA ZALUNTARSU? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 11 November 2017

DOKAR HANA MAKIYAYA YAWON KIYO A JAHAR BENUE KO TAUYE HAƘƘIN MAKIYAYA DA ZALUNTARSU?

Duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya, ya Baiwa kowane dan ƙasa, dama da ikon walwala da zama a inda ya so cikin kasarsa ta gado wato Najeriya.

Sai dai kash! Sannu-sannu wasu gwamnatocin jahohi a Najeriya, suna cigaba da ɗaukar matakai da za su haramtawa, wasu nau'i na al'umma wannan ƴanci da dokar Ƙasa ta ba kowane ɗanta.

Na baya-bayan nan shi ne a ranar Laraba 1-11-2017 da dokar haramta yawo da dabbobi domin kiwo ta fara aiki a jihar Benue.

Wadda dokar za ta tilasta wa dukkan mai kiwo ya tsugunar da dabbobinsa a wuri guda, yayin da ta tanadi daurin shekara biyar ga dukkan wanda ya saba mata.
Har ila yau, wanda ya saba wa dokar zai iya biyan tarar naira miliyan daya a maimakon dauri, ko kuma a daure shi tare da cin tararsa.

Dokar, wadda gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya rattabawa hannu a watan Mayun da ya gabata, ta kuma amince da kafa wuraren kiwo a jihar a, cewarsu.

Bugu da Ƙari Dokar dai ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara biyar ga duk wanda aka samu da laifin kiwo ba a wuraren da aka killace ba, ko kuma tarar naira miliyan ɗaya ko duka biyun.

Haka zalika, a karkashin dokar an haramta yawo da dabbobi da kafa a fadin jihar, sai dai a ɗauke su a kan abin hawa.

Kuma duk wanda aka kama a karon farko za a ci shi tarar naira 500,000 ko daurin shekara daya ko kuma duka biyu.

Wanda aka kama a karo na biyu kuma zai biya tarar naira miliyan ɗaya ko a ɗaure shi ɗaurin shekara uku ko kuma ya fuskanci duka biyun.



Duk wata dabbar da aka gani tana yawo a jihar za a kama ta, in ji dokar.
Idan mai ita bai zo ba bayan mako guda, za a yi gwanjonta ga jama'a kuma a zuba kuɗin a asusun gwamnati. Wannan kenan.

Tabbas duk mai hankalin da ya yi nazarin wadannan dokokin ko matakai tsaurara zai tabbatar da cewa gwamnatin jahar kai tsaye tana yunƙurin korar ƙabilar Fulani makiyaya ne, kwata-kwata daga jahar duk da cewa su kansu 'yan assalin jahar ne.

Kafin Mu je ga ababen da sunka yi hannun riga da kundin tsarin mulkin Najeriya, a cikin wannan bahaguwar dokar.

Zan so in ɗan yiwa gwamnatin jahar wasu 'yan tambayoyi!

Kamar yadda kunka fada cewa; kun dauki matakin ne, domin kawo zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya. To su manoma da ke wawure labi-labi da makiyan su ke biya da shanunsu wane matakin kunka ɗaukar masu?

A cikin wannan Dokar ba ku maida hankali ga manoma ba!

Anya duk wani abu na tashin hankalin da ke faruwa makiyaya dai ne da laifi?

Tunda kun hana yawo da shanu a kasa a duk jahar. A al'adance Fulani daji munka sansu. Kuma ba, a ko ina ba ne mota ke shiga, ya za su yi wajen kai shanunsu a wurin da za su loda su a motar?

Kamar yadda kunka ce kun hana yawo da shanu jahar.

Anya ba ku sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ba da ya bada damar walwala ga 'yan kasa, tare da Baiwa kowane ɗan kasa damar zuwa inda ya ke so cikin ƙasa. Wanda Fulani 'yan kasa ne, suma Suna da damar shiga kowace jaha da shanunsu?

Su baki da ke da tikitin walwala in sun biyo ta jaharku, wane tanadi kunka yi Dan ba su damar wucewa?

Ya Maganar hanyoyin gwamnatin tarayya da ke jahar , za ku iya cewa ba wani bafillanin da zai bi kansu da shanunsa?

Shin wurin kiyon da kunka ce za ku tanadar masu, shin Kafin ku aiwatar da Dokar kun tabbatar da ware bagiren kiyon?

SHARHI!

Matsalar faɗan manoma da makiyaya ba sabuwar Matsala ba ce a ƙasarmu najeriya. Kuma son rai ne, irin na jagororinmu, ya haifar da ita. Musanman na karkara.

Kowa ya tabbatar da cewa tsakanin manoma da makiyaya Ɗanjumma ne da  Ɗanjummai, domin kowanensu yakan ƙaru da wani, kuma akwai matuƙar yadda da fahintar juna a waka-junansu.

Domin makiyayi yakan shiga cikin ƙungurmin daji lokacin da anka shuka kayan goma, da an kai ga amfanin gonar an ɗebe ya dawo su yi yarjeniya tsakaninsu da manomi. Inda zai zauna a gonar manomi yana cin karmami, in ya ƙare ya je wani wajen kiyo. A nan gonar zai yi rani, Har ƙarshensa. Dan haka zai samar da wadataccen taki a gonar.

Amma sannu-sannu saboda son rai irin na jagororinmu. Sun mallakawa manoma Wuraren kiyon dabbobi. Har 'yan burtalolin da da makiyayan ke bi, duk an Nome.

SHAWARA!

Tabbas in dai ana son a kawo karshen wannan matsalar dole gwamnatoci tun daga na Ƙananan hukumomi, jaha da kuma tarayya su shigo.

Na farko dai, in Har ba a iya zamanantar da sha'anin kiyon, ta yadda makiyaya za su zama waje ɗaya su yi sana'arsu tare da ilmantar da su, Kamar yadda ake yiwa sauran 'yan Najeriya.

To a tabbatar an samar da muhimmin gandun daji, mai yalwa da makiyaya za su yi kiyon dabbobinsu. Haka zalika a tabbatar da cewa burtullan makiyaya an inganta su tare da fadada su, ta yadda makiyayan za su iya yin kiyonsu ba tare da sun shiga gonar Kowa ba.

Bayan anyi Haka sai a sanya hukumar da za ta rinka kula da duka bangarorin, Dan tabbatar da manoma ba su ci burtalolin ko gandun dajin ba, haka suma makiyaya ba su shiga gonar manoma ba. Wanda duk anka Kama wani da laifi a yi masa hukunci mai tsanani. Muddun anka yi haka da ikon Allah, za a ji saukin wannan matsalar.

Dan haka muna kira ga ita gwamnatin jahar Benue da ta dauki matakin da zai yuyu domin maganin wannan matsalar, amma ba Dai wannan da sunka dauka yanzu ba, domin Dai Wallahi wannan Dokar ba abunda za ta yiwa Jahar sai dai ta jefa ta cikin halin ƙaƙa-ni-kayi. Tare da jefa Al'ummar jahar cikin halin ɗar-ɗar.

Daga ƙarshe muna rokon Allah ya kawo muna ƙarshen duk wasu tashe-tashen hankulla a ƙasarmu Najeriya. Tare da dora ƙasarmu akan yalwar arziki marar yankewa

Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulɗa Da Jama'a Na Ƙungiyar Muryar Talaka Ta Ƙasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

11-11-2017

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here