Assalamu alaikum, bayan gaisuwa tare da fatan kana cikin koshin lafiya.
Kai tsaye yau mun rubuta maka wannan wasika ce, cikin ladabi tare da kokarin sanar da kai wani Wata aika-aikar da Mu ke da yakinin baka san da ita ba. Wanda kai daya ne zaka iya magance wannan matsalar ko in ce daukar matakin daya dace. Domin ceto Al'ummar RIJIYAR GABAS da ke Nan cikin garin GUSAU.
Ya mai girma gwamna za mu so ka Dan natsu, ka saurare mu tare da share muna hawayenmu, domin muna da yakinin baka san abunda ke faruwa ba. Wanda muna tunanen in ka sani za ka iya share wa Al'ummar hawayensu, Kamar yadda nauyi ya taraya wuyanka;
Mai girma gwamna al'ummar Unguwar Rijiyar Gabas 86 Housing Estate (extension) bypass Gusau. Sun tsinci kansu cikin wani rudani sakamakon,
Ganin an Fara cike wani fili da ruwa ke kwanciya tare da yunkurin sana'anta duk wani fili na daura da shi a unguwar wanda kacokan, ai'nihi wurin An ware shi domin yin makaranta (based on master plan) na unguwar tare da 'yan kasuwa domin bunkasa walwala da jin dadin mazaunanta. Da yake unguwar ta kananan ma'aikata ce ba za su iya gina shi da kansu ba.
Wanda kanenka ALH JAFARU ABUBAKAR YARI T/MAFARA (DAN AUTA) Ya ce wannan wuri mallakarsa ne ya saya ne a kotu ga magadan ALH SHEHU BAKAUYE. Duk da cewa shekara biyu da suka wuce mai girma Gwamna da kanka ka yi alkawarin gina hanyoyin unguwar. Wanda zuwa yanzu dai Allah bai baka ikon yi ba.
Sai ga shi yanzu kanenka ya bi wasu hanyoyi an mallaka masa hanyoyin da da filin makaranta.
Ya mai girma gwamna wannan fili muddun anka ce za a gina shi ko a mallakawa wani shi to tamkar an tarwatsa Al'ummar unguwar ne. Domin baki daya za a rufe masu hanyoyin da ke Sada su da gidajensu. Haka zalika za su rasa filin da za a yi masu makaranta zuwa gaba, dama karamar kasuwa, Kamar yadda anka samar da filin Dan yi.
Hakika wannan Kane naka yafi karfin wannan fili, ya mai girma gwamna. Bakin gwargwado muna tunanen in ka San abunda zai yi ya cutar da al'ummarka zaka iya taka masa burki a tunanenmu.
Dan haka ya mai girma gwamna, muna da yakinin zaka ji kokenmu. Muna neman alfarmar ka dakatar da wannan Kane naka daga cigaba da wannan aiki da ya dauki aniyar yi. Wanda na tabbatar yinsa zai jefa al'ummarka cikin kunci na illamasha'allah.
Daga karshe muna rokon Allah ya sa wannan koke namu ya kai ga kunnuwan da munka yi domin su, ya kuma ba ka ikon share muna hawayenmu.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara)
9-11-2017





