Jiya lahadi 5-11-2017 ne Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Zamfara ta halarci wani gagarumin aikin gayya wanda Al'ummar sankalawa da ke karamar hukumar mulki ta bungudu, sunka shirya.
Aikin gayyar dai ya samu halartar Shuwagabanni da membobin kungiyar muryar talaka reshen Jahar Zamfara.
A lokacin da ya ke jawabi, Shugaban Kungiyar na jaha Kwamrad Hafizu Balarabe Gusau wanda shi ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa gurin wannan aikin gayyar ya bayyana aikin gayya a matsayin daya daga cikin ayukkan kungiyar muryar talaka, kuma ya sha alwashin 'ya'yan kungiyar za su cigaba da halartar irin wadannan ayukkan Dan cigaban kasa.
Haka zalika da ya ke tsokaci babban uban Kasar wannan yankin. Ya nuna jin dadinsa matuka ga kwazon kungiyar Muryar Talaka na halartar wannan aikin, la'akkari da rashin kyawon hanya da nisa duk basu hana 'ya'yan kungiyar zuwa wajen aikin ba. Bugu da kari ya roki Allah ya cigaba da yiwa kungiyar jagoranci nagari.
Da ya ke rufe taron da jawabinsa, sakataren kungiyar Activist Muhammad Lawal Gusau. Ya sha alwashin cewa kungiyar muryar Talaka za yi duk mai yuyuwa wajen kai koken Al'ummar domin gwamnati ta samar masu da titi, musanman ganin yadda yankin yake da matukar yabanyar noma. Wanda yi masu hanyar zai taimaka wajen habbaka arzikin yankin dama jahar Zamfara baki daya.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. Pro 1 Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara.

