AN KASHE BUHARIN DAJI, NI KAINA NAGA GAWAR DA IDANU NA, DOMIN HAR KURA TA FARA CIN CINYARSA, KAFIN DAUKO GAWAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 9 March 2018

AN KASHE BUHARIN DAJI, NI KAINA NAGA GAWAR DA IDANU NA, DOMIN HAR KURA TA FARA CIN CINYARSA, KAFIN DAUKO GAWAR.



Buharin daji, wani kasurgumin Barawon shanu ne, da ya yi suna wajen satar shanu dama kisan Al'umma Musamman na Karkarar Jahar Zamfara

An dade ana bayar da rahotanni akan cewa an kashe shi. Daga baya Kuma a ce ba shi ne anka kashe ba. Sai Dai yanzu Alhamdulilahi an rage mugun iri.

Domin tuni wannan bakin azzulumin ya sheka barzahu, domin ni kaina ina cikin tarin 'yan jaridu da 'yan Social Media dinda anka baiwa damar Ganinsa tare da daukar hotonansa (in kunka bi turaka ta facebook za ku ga yadda na kawo abun kai tsaye.)

An dai kashe wannan bakin barawon ne, awanni kasurgumin da ke DANSADAU ta Karamar hukumar mulkin Maru.

Muna rokon Allah ya sa kashe wannan bawan Allah ya taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaron Jahar Zamfara baki daya.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

9-3-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here