Kamar yadda Kungiyar MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA ta shirya zaben jin ra'ayin jama'a akan Wanda ya dace ya zama tsakanin wasu muhimman mutane biyar a Jahar Zamfara.
ENGR. ABU MAGAJI Bayan ya zama Babban Sakataren gwamnatin tarayya, an shede shi da kyakkyawan hali da riko da addinin isalama da ma son talakkawan da ya ke cikinsu.
Domin karrama shi tare da kara masa karfin guiwar cigaba da yiwa al'ummarsa ayukkan azo a gani. Wanda Hakan zai kara karfafa takwarorinsa, wajen kula da Al'umma.
la'akkari da wadannan hujjoji kamar haka da al'umma sunka fada akan wannan SAKATARE ;
BANGAREN NEMAN ILIMI.
√ Computer Guda Dari (100) ZACAS
√ Gina Block Daukancin Kananan Hukumomin Goma Sha Hudu Dake Zamfara.
√ Dauka Nauyi Daliban Hamsin Da Shida 56 Makarantar FUG Gusau.
√ Ya Bada Tallafi Ga Marasa Galihu Domin Su Cigaba Da Karatun Su a Manyan Makarantun Kasar nan Da Binin Republic.
BANGAREN KIYON LAFIYA.
Ya Dauki Nauyin Bada Maganin Kyauta Ga Mata Dari Hudu (400) Dake Kananan Gusau,Tsafe, da Kauran Namoda.
Dauka Nauyi Marasa Lafiya.
Ya Bada Generator Ga Asibitin Yarima Bakura Da ke Nan Gusau.
Ya Bada Tallafin Kayan Aiki ga Daukacin Masarautu Goma Sha Bakwai Dake Zamfara.
BANGAREN SAMAR DA RUWAN SHA.
ya g Gina Da Samarda Da Bohole na Samar da Ruwan Sha A Garuruwan Bukuyyum, Anka da Maroki da Wasu Unguwanin Dake Cikin Garin Gusau.
SAMAR DA AYUKKAN YI.
Ya Samarwa Matasan Aikin A Matakin Gwamnatin Tarraya da Sun ka Hada Civil Defence,Road Sefety,Prison Sevice,Custom,Imagaration,Police, Air Force Land Amy,Neavy, Federal Fire Service da Kuma Ayyukan Office.
Wutar Lantarki.
Ya Samarda Manya Transformer 500KV A Garuwan Bukuyum,Maru da Shinkafi da Wasu Unguwanin da Cikin Garin.
Mata.
Ya Kawo Mace (600) Sana'a in Hannun tare da Basu Tallafi Abun da Sun Ka Koya.
Hanyoyin Da Gadoji.
Samar Da Gyaran Titin Futuwa Zuwa Sokoto
Samar Da Gada A Hanyin Malam Sani Garin Gusau
Samar Da Gada Yar dantsi
Samarda Tagawaayen Gadojin A Manyanchi da Kaudari.
Samar da Aikin Hanya Gusau Zuwa Rijiya 22 Kilo Meters.
Addinin.
Gina Ajujuwan Karatun tare Bohole na Ruwa Sha CIBIYAR Uthamis Dake Gusau.
Gina Makarantar Isamiyya Fadar Mairtaban Sarkin Zamfara Anka.
Gina Makarantar Islamiyya Garin Bukkuyum.
Gina Makarantar Makarantar Isalamiyya A Kaura Nomoda.
Gina Block A Makarantar Islamiyya tare Da Ruwa Sha A Unguwar Gwaza.
Gina Makarantar Shiyar Kamfala.
Gyara Makarantar Islamiyya da Masalacin Zuwa Ginin Zamani Shirya Filin Tanko.
Gina Masalacin Shiryar Unguwar Yarima.
la'akkari da wadannan kwakkwaran dalillai da kyakkyawan ayukkan, Kungiyar MURYAR TALAKA ta yi Dogaro. Har ta aminta da cewa shi ne ya zo na biyu a tsakanin dukkannin takwarorinsa biyar a Jahar Zamfara, Dan Haka zata baiwa wannan Dan tahalikin Lambar YABO a Babban taron Kungiyar da za ta yi a watan 3-2018 a Matsayin Kwarzon SHEKARA || na Zamfara.
Muna Taya shi ENGR. ABU MAGAJI GUSAU, murna, Allah ya ba shi ikon cigaba da yiwa Al'ummarsa abubuwan kirki, muna rokon Allah ya sa wannan Karramawar ta kara masa azama. Daga karshe muna rokon Allah ya daukaki shi a fagen aikinsa dama siyasar da zai fara domin cigaba da yiwa Al'umma hidima.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA. A madadin dukkanin shuwagabannin Kungiyar da membobinmu.

