SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA DR. ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARIN A MATSAYIN GWARZON SHEKARA NA ZAMFARA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 14 March 2018

SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA DR. ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARIN A MATSAYIN GWARZON SHEKARA NA ZAMFARA!



Kamar yadda Kungiyar MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA ta shirya zaben jin ra'ayin jama'a akan Wanda ya dace ya zama tsakanin wasu muhimman mutane biyar a Jahar Zamfara.

GWAMNA ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA Bayan ya zama Zababben gwamnan Jahar Zamfara, an shede shi da riko da addinin isalama da ma dakewa akan Abunda ya yarda da shi, tare da baiwa 'yan adawa damar yin adawarsu ba tare da tsangwama ba.

Domin karrama shi tare da kara masa karfin guiwar cigaba da yiwa al'ummarsa ayukkan azo a gani. Wanda Hakan zai kara karfafa takwarorinsa, wajen kula da Al'ummarsu.

la'akkari da wadannan hujjoji kamar haka da al'umma sunka fada akan wannan GWAMNA; ( a latsa bulan rubutun da ke kasa)

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=921818904650530&id=100004672867698


Da wadannan kwakkwaran dalillai da kyakkyawan ayukkan, Kungiyar MURYAR TALAKA ta yi Dogaro. Har ta aminta da cewa shi ne ya zo daya a tsakanin dukkannin takwarorinsa biyar a Jahar Zamfara, Dan Haka zata baiwa wannan Dan tahalikin Lambar YABO a Babban taron Kungiyar da za ta yi a watan 3-2018 a Matsayin Kwarzon SHEKARA na Zamfara.

Muna Taya shi GWAMNA ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI, murna, Allah ya ba shi ikon cigaba da yiwa Al'ummarsa abubuwan kirki, muna rokon Allah ya sa wannan Karramawar ta kara masa karfin guiwar cigaba da yiwa al'ummarsa abun azo a gani.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA. A madadin dukkanin shuwagabannin Kungiyar da membobinmu.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here