TASHIN HANKALIN DA KE TAFE GA AL'UMMAR JAHAR ZAMFARA .... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 9 March 2018

TASHIN HANKALIN DA KE TAFE GA AL'UMMAR JAHAR ZAMFARA ....


Na Dauki wannan Yaron hoto, a nan KAMBARI PLAZA, Tashar Bagu Gusau. Yau.

Duk Wanda ya kula zai ga cewa kayan Makaranta ne, wannan Yaron ya ke saye da su. Amma ya ki zuwa makarantar, ya zo nan shagon da ake CACA (BET9JA) zai yi.

Ba ni tunanen wannan Yaron ya kai shekaru goma a duniya.

Akalla da na shiga cikin shagon na tarar da Yaran da sunka ki zuwa makarantar sun kai biyar, ba daya daga cikinsu da ya kai shekaru goma sha takwas!

Mu kula wadannan Yaran su ne, manyan gobe, Anya in munka zura ido a haka, za mu samu al'umma ta gari a gaba?

Abinda ya kamata mu kula a nan shi ne; duk yaran da ke barin makarantar Suna zuwa wajen wannan CACAR 'ya'yanmu ne, kannenmu ne, Hausawa. Wallahi ban taba ganin ko da matashin da ba namu ba yazo wajen yinta.

Mu kula wasunmu NE, sunka kawo muna ita, sun tura 'ya'yansu da kannensu makaranta da koya masu sana'o'i. Amma  Dan rashin hankali irin namu mun basu hayar Shago, dan su lalata muna rayuwar Al'umma!

Wanda ke da SHAGON wannan CACAR, yiwa kasa hidima (Service)  ya zo a Jahar Zamfara. A madadin ya yi muna hidimar da za ta ciyar da mu gaba, ya buge da hidimar halakar da mu, ya kammala yiwa kasar hidima ya fara yiwa kungiyoyinsu na YAHUDAWA hidima.

INA MAFITA!

Tunda ita gwamnatin Jahar Zamfara bata da gudurin  ta tashi tsaye wajen, hana wanan annobar. To dole mu Al'ummar Jahar Zamfara mu tashi tsaye ta hanyar daukar doka a hannunmu, ma'ana masu shagunan haya su dena bayarwa. Mu Kuma da ke zagaye da masu shagunan mu sanya ido duk Yaron da munka yi arba da shi zai yi wannan CACAR muna hana shi, in ya ki ji, mu hukunta shi ta hanyar da zai sa gobe ba zai dawo ba.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
9-3-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here