Shehin Malami Dan Assalin jahar Kebbi, Wanda yanzu haka, shi ne Shugaban Tsangayar ilimi da Nazarin zamantakewar da Adam a Jami'ar Gwamnatin tarayya da ke Gusau, Kuma Shugaban sashen al'addu da Harsuna na jam'iya. Ya bayyana cewa gwamnatin jahar Zamfara ta tabka wannan mantuwa NE, a wani Gaggarumin biki da kungiyar Dalibban jahar Zamfara suka shirya a ranar Lahadi 17-6-2018 wanda Shehin malamin a ya Gabatar da Lecture mai taken "KUNYA GINSHIKIN TSARON KASA DA BUNKASARTA"
A lokacin da ya kawo karshen lecture tasa ya bayyana cewa;
"Hakika Gwamnan jahar Zamfara mai ci a yanzu ya yi wa Zamfarawa abunda ba wani gwamna da ya taba yi masu shi, domin ko haka dai ya tsaya a jami'ar da kafa a Talatar Mafara, ya biya Zamfarawa Sauran Sunnah NE, Allah ya saka masa da alheri. Sai dai kash! Ina ganin Gwamnatin jahar Hakika ta yi Gagarumar mantuwa, domin rashin Sanya Manhajar Nazarin harshen Hausa da ba a yi a cikin wannan jami'ar ba. Babbar mantuwa ce, da ina ganin farfesa Birbis ya yi, domin jami'ar nan ba dan kowa aka yi ta ba, sai dan zamfarawa. A tuna jahar Zamfara Akwai farfesa biyar Dukkaninsu Hausa suka karanta
"Domin na tabbatar idan ba mantuwa ba ba yadda za a ki Sanya harshen Hausa a cikin yarukkan da za a koyar a cikin wannan Jami'ar. Domin muhimmancin harshen mutun ya sa idan ka shiga Dukkanin Jami'o'in Saudiya Sai ka tarar akwai bangare na musamman na Nazarin harshen Larabci, Amurika, China, Faransa Jamus Dukkanin Jami'o'insu ba Wadda bai zama dole a sanya Manhajar Harsunan kasashen a Jami'o'insu ba.
"Amma abun Mamaki a Najeriya, a Arewa, uwa-uba a jahar Zamfara, a yi Jami'a sukkutum! Amma wai ba a Sanya harshen Hausa a cikin yarukkan da za a bude jami'ar da su, ba. Hakaki Gwamnatin jahar Zamfara ta yi mantuwa. Kuma ina amfani da wannan damar in yi tunatarwa ga Gwamnatin zamfara da Shugaban kwamitin kirkirar Jami'ar wato farfesa Birbis, Wanda Alhamdulillahi, wakilinsa na nan.
"Domin Maganar Gaskiya babbar mantuwa ce la'akkari da wannan harshen Dari-bisa-dari shi ne na al'ummar jahar Zamfara da shi su ke magana. In ko haka ne, in harshe daya za a koyar to ya dace harshen Hausa ne.
"Idan muka duba a majalissar dokokin jahar zamfara da Hausa ake magana, a Dukkanin fadodin sarakunan Zamfara da Hausa ake Magana, Duk inda gwamnan jahar Zamfara ya yi magana, in dai akan jahar Zamfara ya yi ta Sai ya dawo ya fassara ta zuwa Hausa, Dan sannin al'ummarsa hausawa NE, Kuma ya yi maganar ne Dan su.
"Anya kuwa?
"Dan haka muna kira ga wannan kwamitin da da ita Gwamnatin jahar Zamfara da su dauki matakin gyara wannan Gagarumar mantuwa da suka yi."

