ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JAHARMU: KO KA SAN SAKAMAKON JARABAWAR WAEC DA NECO YA FITO? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 24 August 2018

ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JAHARMU: KO KA SAN SAKAMAKON JARABAWAR WAEC DA NECO YA FITO?



kamar yadda ka sani (a tunanenmu) an Sako sakamakon Jarabawar WAEC ta 2018 wanda tuni da dama daga cikin dalibban da suka rubuta ita wannan Jarabawar a makarantanni masu zaman kansu da sauran jahohin da ke kishin cigaban al'ummar jaharsu (domin Duk wanda bai kishin cigaban ilimi, baya kishin al'ummarsa).


Haka zalika ga NECO ta fito itama tuni wadanda na fada a sama sun duba nasu sakamakon. Har sun shiga sawun masu kokarin komawa makaranta. Amma 'ya'yan masu Dan karamin karfi na nan ba su san makomarsu ba. 


Kusan in ce, mu ne dalibbai na farko da suka fara dandanar kudarsu a yayin wannan mulkinka. Haka aka yi ga na bayanmu har zuwa yau.

Dan haka ina amfani da wannan damar in yi kira gareka da ka ji tsoron Allah ka yi kishin cigaban ilimin al'ummarka, kamar yadda ka ke yin na 'ya'yanka. Ko ba komi wannan shi ne biya na karshe da gwamnatinka za ta yi. Dan haka ya kamata ko Dan badi mu tuna ka da alheri. Ka yi kokarin biyan wadannan kudaden Dan ceton jaharka. Domin rashin biyan kan-kari na daya daga cikin ababen da ke sa wasu dalibban na dena karatun baki daya.


Allah ya sa kiran nawa ya Kai ga kunnuwan wanda na yi dominsa.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.


24-8-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here