Gidauniyar shugaban Matasan jam'iyar Apc ta jahar Zamfara, ta kaddamar da aikin tallafi a Babban zawuyyar Gusau.
Da mu ke zantawa da jagoran Gidauniyar Kuma Kane da mamallakin Gidauniyar Malam. Shafi'u Sani Malolo Ya bayyana cewa; "mun zo wannan Makarantar NE, domin kaddamar da wannan aikin alheri. Kuma za mu cigaba da yinsa lungu da Sako na jahar Zamfara, domin bayar da ta mu gudunmawa ga masu Dan karamin karfi. Musamman almarai."
Da mu ke tambayarsa wane tallafi ne, Gidauniyar ta kawo?
Malolo ya ce; " mun kawo Sabulun wanki da na wanka da man shafawa da omo, Tare da yin FESHIN maganin sauro a wannan makaranta Dan Yakar zazzabin cizon sauro da ke jefa almajiran cikin halin kaka-ni-ka-yi. Sauran kayan Kuma Dan tsaftace Kai da suturun almajiran.
"Kuma Insha Allahu za mu gaba da yin hakan, Fatanmu dai aikin namu ya kai ga Mizanin ayukkan mu nagari, haka ya kamata sauran al'umma su ma su shigo cikin irin wannan aikin jinkan. "

