Idan na ce jami'an Tsaron Najeriya ina nufin Duk wata hukuma da ke da hannun wajen samar da Tsaro. Hakika kun yi kokari jiya wajen samar da Tsaro a jahar Zamfara, Musamman jami'an DSS da su ne suka yi nasarar kwantar da tanzomar da ta kai ga KONE-KONEN tayoyi!
Hakika kun ga abunda ya faru jiya, Musamman KASHE-KASHEN rayukka da ya faru a jahar Zamfara, Duk da sunan zaben YAR-TIKE NA JAMI'IYAR APC!
Akinku ne ku yi bincike akai ba tare da wani ya tsoma maku baki ba. Haka zalika aikin ku a kullum ku yi kokarin Kare rayukkan jama'a da dukiyoyinsu, haka Duk wani yunkuri na tada zaune tsaye, Kuna kokari matukar gaske wajen ganin an shawo kan rikicin in ya auku, kafin ya auku Kuma ku yi kokarin toshe shi.
Alhamdulillahi da dama kungiyoyi da gwamnatoci sukan yin kokarin aiwatar da wani Abu, saboda hasashen barkewar tarzoma ku hana Dan ganin an samu fahintar juna da zama Lafiya a cikin al'umma, Tunda haka ne. Hakika ya zama wajibi gare da ku Kalli Duk wani yunkuri na Gwamnatin jahar Zamfara ke yi, musamman na gudanar da zaben da ta ce za yi yau. Kuma Wai fa a cewar tare da ku....
Nasan ku ba 'yan siyasa ba ne, Kuma ba za ku yarda ayi amfani da ku wajen biyan wata bukata ta wanin Dan siyasa da za ta kawo rashin zaman lafiya ba, Dan haka muna kira gareka ku da ku tabbatar kun hana mai girma gwamna shirya zaben da ya ce zai yi yau.
haka zalika ku tabbatar kun Rubutawa uwar jam'iyar APC rahoto akan matsalolin da kuka gani wajen aiwatar da wannan zaben, kamar yadda kai tsaye wani bangare ke kokarin tada zaune tsaye, da kuma almudana.
Tare da tabbatar da cewa ba a sake yin wani zaben YAR-TIKE din ba, Sai an tabbatar da cewa; an kawo wadatattun jami'an Tsaron da za su iya bayar da Tsaro wajen zaben, tare da tabbatar da an yi zaben Lafiya an Kammala Lafiya.
Allah ya sa a yi wannan zaben Lafiya, a Kammala Lafiya. Allah muna rokonka ka arzurtamu da Shugaba adili wanda zai jagoranci bunkasar tattalin arziki da cigaban jahar Zamfara baki daya.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
4-10-2018

